23
Sai duk taron suka tashi, suka kawo Yesu gaban Bilatus. Suka fara saransa, cewa “Mun same wannan mutum yana ruda kasarmu, ya haramta a ba Kaisar haraji, yana kuma cewa shi da kansa ne Almasihu, sarki.” Bilatus ya tambaye shi, cewa “Shin kaine Sarkin Yahudawa?” Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Haka ka ce.” Sai Bilatus ya ce wa manyan firistocin da taro mai yawa, “Ban samu ko laifi daya game da wannan mutumin ba.” Amma suka yi ta cewa, “Yana ta da hankalin mutane da koyarwa a dukan Yahudiya, ya fara daga Galili har zuwa ga wannan wuri.” Sa'adda Bilatus ya ji wannan, sai ya tambaya ko mutumin daga Galiline. Sa'adda ya gane cewa yana karkashin mulkin Hirudus, sai ya tura Yesu wurin Hirudus, wanda shi da kansa yana Urushalima a wadannan kwanakin. Sa'adda Hirudus ya ga Yesu, sai ya cika da farin ciki sosai, saboda ya so ganinsa tunda dadewa. Tun can ya ji game da shi sai ya yi begen ganin wadansu al'ajibai da zai yi. Hirudus ya tambaye Yesu cikin kalmomi masu yawa, amma Yesu bai amsa masa da komai ba. 10 Sai manyan firistoci da marubuta suka tsaya, suna ta yi masa zargi mai zafi. 11 Hirudus da sojojinsa suka zarge shi, suka kuma yi masa ba'a, suka sa masa tufafi masu kyau, sa'annan ya sake aika Yesu zuwa wurin Bilatus. 12 Sai Hirudus da Bilatus suka zama abokai a wannan rana (da ma su abokai gaba ne). 13 Bilatus ya kira manyan firistoci tare da masu mulki da kuma taron jama'ar, 14 sai ya ce masu, “Kun kawo mani wannan mutum kamar wanda yake jagorar mutane ga munanan ayyuka, ku kuma gani, Ni, na tuhume shi a gabanku, ban sami ko kuskure daya daga mutumin nan game da abinda ku ke zarginsa da shi ba. 15 Babu, ko Hirudus ma, ya sake komar mana da shi, kun gani, babu wani abu wanda ya yi da ya cancanci mutuwa, 16 saboda haka zan yi masa horo sa'annan in sake shi.” 17 [Ya zama dole Bilatus ya sakar wa Yahudawa wani daurarre guda daya lokacin idin.] 18 Amma dukansu suka yi ihu tare, cewa, “A tafi da wannan mutumin, sai a sako mana Barabbas!” 19 Barabbas mutum ne wanda aka sa a cikin kurkuku saboda wani tada hankali a cikin birni da kuma kisankai. 20 Bilatus ya sake yi masu magana, yana so ya saki Yesu. 21 Amma suka yi ihu, cewa, “A giciye shi, a giciye shi.” 22 Sai ya sake ce masu sau na uku, “Don me, wace magunta wannan mutum ya yi? Ban sami wani abu da ya isa sanadin mutuwa game da shi ba. Saboda haka bayan na hore shi, zan sake shi.” 23 Amma suka nace da murya mai karfi, suna so a giciye shi, sai muryarsu ta rinjayi Bilatus. 24 Sai Bilatus ya yarda ya yi masu bisa ga abin da suke so. 25 Ya sako masu wanda suka tambaya ya ba su wanda aka sa a kurkuku domin tada hankali da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu bisa nufinsu. 26 Da suka tafi da shi, sai suka kama wani mai suna siman Bakurane, yana zuwa daga karkara, sai suka daura masa giciyen ya dauka, yana biye da Yesu. 27 Babban taron jama'a, da na mata da suke makoki da kuka dominsa, suna binsa. 28 Amma da ya juya wurinsu, Yesu yace, “Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka domina, amma ku yi kuka domin kanku da 'ya'yanku. 29 Gama ku gani, kwanaki suna zuwa da za su ce, 'Albarka ta tabbata ga bakararru da wadanda basu taba haihuwa ba da kuma wadanda ba a taba shan mamansu ba.' 30 Sa'annan za su fara ce wa duwatsu, 'Ku fado bisanmu,' da tuddai ma, 'Ku rufe mu.' 31 Gama idan sun yi wadannan abubuwan lokacin da itace yana danye, me zai faru sa'adda ya bushe?” 32 Aka kai wadansu mutum biyu masu laifi, domin a kashe shi tare da su. 33 Sa'adda suka zo wurin da a ke kira kwalluwa, nan suka giciye shi da barayin, daya daga hannun damansa dayan kuma daga hannun hagu. 34 Yesu yace, “Uba, ka yafe masu, gama basu san abin da suke yi ba.” Sai suka jefa kuri'a, suka rarraba tufafinsa. 35 Mutane sun tsaya suna kallo sa'annan masu mulki suna ta yin masa ba'a, cewa, “Ya ceci wadansu. Bari ya ceci kansa, idan shine Almasihu na Allah, zababben nan.” 36 Sojojin ma suka yi masa dariya, suna zuwa wurinsa, suna mika masa ruwan tsami, 37 suna cewa, “Idan kai Sarkin Yahudawa ne, ceci kanka.” 38 Akwai wata alama bisansa, “Wannan shine Sarkin Yahudawa.” 39 Daya daga cikin barayi wanda aka giciye, ya zage shi, cewa, “Ba kai ne Almasihu ba? Ka ceci kanka da mu.” 40 Amma dayan ya amsa, ya tsauta masa cewa, “Ba ka tsoron Allah, da yake shari'arka daya ne da nasa? 41 Mu kam an yi ma na daidai, gama mun samu bisa ga abin da muka yi. Amma wannan mutum bai yi wani abu mara kyau ba.” 42 Sai ya kara, “Yesu, ka tuna da ni sa'adda ka shiga mulkinka.” 43 Yesu ya ce masa, “Gaskiya ina ce maka, yau za ka kasance tare da ni a firdausi.” 44 Anan nan a wajen sa'a na shida, sai duhu ya mamaye kasar duka har zuwa sa'a na tara 45 sa'adda rana ya fadi. Sai labulen haikalin ya rabu a tsakiya zuwa kasa. 46 Da kuka da murya mai karfi, Yesu yace, “Uba, na mika Ruhu na a hannunka.” Bayan da ya fadi wannan, sai ya mutu. 47 Sa'adda jarumin ya ga abin da ya faru, ya daukaka Allah, cewa, “Lallai wannan mutumin mai adalci ne.” 48 Sa'adda dukan taro mai yawa wadanda suka zo tare domin su shaida da idanunsu suka ga abubuwan da suka faru, suka koma suna bugan kirjinsu. 49 Amma duk idon sani, da kuma matan da suka bi shi tun daga Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban wadannan abubuwa. 50 Ga shi kuwa, wani mutum mai suna Yusufu, shi dan majalisa ne, nagari ne kuma mutum mai adalci ne 51 (bai yarda da shawarar da kuma abin da suka aikata ba), daga Arimatiya a kasar Yahudiya, wanda yake jiran mulkin Allah. 52 Wannan mutum, ya sami Bilatus, ya tambaya a bashi jikin Yesu. 53 Ya saukar da shi kasa, sai ya nade shi cikin likafani na linin mai kyau, ya kwantar da shi cikin kabari da aka sassaka shi daga dutse, inda ba a taba binne wani ba. 54 Ranar kuwa, ranar shiri ce, Asabaci kuma ta kusato. 55 Matan da suka taho da shi tun daga Galili, suka biyo baya, su ga kabarin da inda aka ajiye shi. 56 Suka koma, sai suka shirya kayan kamshi da mai. Suka kuma huta a ranar Asabaci bisa ga doka.