7
1 Bayan da Yesu ya gama fadar dukan abubuwan da zai fadi a jin kunnen dukan mutanen, sai ya shiga Kafarnahum.
2 Bawan wani jarumi, wanda yake kauna, ba shi da lafiya har ma ya kusa mutuwa.
3 Amma da ya ji labarin Yesu, jarumin ya aiki wadansu dattawan Yahudawa, ya ce a roki Yesu ya zo ya ceci bawansa daga mutuwa.
4 Sa'adda su ka zo kusa da Yesu, su ka roke shi da gaske, cewa, “Wannan ya isa ka yi masa haka,
5 saboda shi mai kaunar kasar mu ne, kuma shi ne ya gina mana majami'a.
6 Sai Yesu ya tafi tare da su. Amma sa'adda ya zo kusa da gidan mutumin, jarumin ya aiki abokansa su ka ce da shi, “Ubangiji kada ka damu domin ni ban isa ka zo gida na ba.
7 Shi ya sa na ga ban isa in zo wurinka ba, ka yi magana kadai bawa na kuwa zai warke.
8 Gama ni ma mutum ne mai iko, ina da sojoji karkashina. Ina iya cewa da wannan, 'Ka je' sai ya tafi, in kuma ce da wani 'ka zo' sai ya zo, in kuma ce da bawa na, 'Yi kaza,' sai ya yi.”
9 Sa'adda Yesu ya ji haka, ya yi mamakin mutumin, ya juya wajen taron da su ke biye da shi, ya ce, “Na gaya maku, ko a cikin Isra'ila ban sami wani mai bangaskiya irin wannan ba”
10 Daga nan wadanda a ka aika, suka dawo gida suka tarar da bawan cikin koshin lafiya.
11 Wani lokaci bayan wannan, ya zama Yesu yana tafiya wani gari da ake kira Na'im. Almajiransa su na tare da shi, da kuma taron mutane masu yawa.
12 Sa'adda ya kusa da kofar garin, sai ga wani matacce ana dauke da shi. Kuma shi kadai ne da a wurin mahaifiyarsa. Ita kuwa gwauruwa ce, mutane da dama daga cikin gari suna tare da ita.
13 Da ganin ta, sai Ubangiji ya cika da tausayi a game da ita ya ce da ita, “Kada ki yi kuka.”
14 Sai ya zo ya taba makarar, sai masu dauke da shi su ka tsaya. Ya ce 'Saurayi na ce ma ka ka tashi.”
15 Sai mataccen ya tashi ya fara yin magana. Sai Yesu ya ba mahaifiyar danta.
16 Sai tsoro ya kama su duka. Su ka kama yabon Allah, su na cewa, “An ta da wani annabi mai girma a cikinmu” kuma “Allah ya dubi mutanensa.”
17 Wannan labari na Yesu, ya ba zu a cikin dukan Yahudiya da yankuna da su ke kewaye.
18 Almajiran Yahaya suka gaya masa dukan wadannan abubuwa.
19 Sai Yahaya ya kira biyu daga cikin almajiransa, ya aike su wurin Ubangiji, suka ce da shi, “Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?”
20 Sa'adda suka zo kusa da Yesu, sai mutanen suka ce, “Yahaya Mai Baftisma, ya aiko mu, mu tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?”
21 A cikin wannan lokaci, ya warkar da mutane da yawa daga cututtuka da matsaloli da miyagun ruhohi. Makafi da yawa sun sami ganin gari.
22 Yesu, ya amsa ya ce masu, “Bayan kun tafi, ku ba Yohanna rahoton abin da ku ka ji da abin da ku ka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana kuma tsarkake kutare. Kurame suna ji, ana tayar da matattu, ana gaya wa matalauta labari mai dadi.
23 Mai albarka ne mutumin da ya tsaya a kan ba da gaskiya gare ni saboda ayukan da na ke yi.”
24 Bayan da mutanen da Yahaya ya aiko suka tafi, Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yahaya. “Me ku ka tafi ku gani a cikin hamada, ciyawa wadda iska ta ke girgizawa?
25 Amma me ku ka tafi domin ku gani, mutum mai saye da tufafi masu taushi? Duba mutanen da su ke saye da tufafi masu daraja, kuma suna rayuwa cikin jin dadi suna fadar sarakuna.
26 Amma me ku ka tafi domin ku gani, annabi ne? I, ina gaya ma ku, ya ma fi annabi.
27 Wannan shine wanda aka rubuta a kansa, “Duba, ina aika manzo na a gabanka, wanda za ya shirya maka hanya a gabanka.
28 Ina gaya maku, a cikin wadanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka, wanda ya fi kankanta a mulkin Allah, ya fi shi girma.
29 Sa'anda dukan mutane suka ji haka, har da ma su karbar haraji, suka shaida Allah mai adalci ne. Su na cikin wadanda Yahaya ya yi wa baftisma.
30 Amma Farisawa da wadanda su ke kwararru a cikin shari'ar Yahudawa, wadanda ba shi ne ya yi masu baftisma ba, suka yi watsi da hikimar Allah don kansu.
31 Sa'annan Yesu ya ce, “Da me zan kamanta mutanen wannan zamani? Da me suka yi kama?
32 Suna kama da yaran da suke wasa a kasuwa, wadanda suke magana da junansu suna cewa, “Mun yi maku busa, ba ku yi rawa ba. Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba.”
33 Haka, Yahaya ya zo, bai ci gurasa ba, bai sha ruwan inabi ba, amma ku ka ce, 'Aljani ne yake mulkinsa.
34 Dan Mutum, ya zo, yana ci, yana sha, amma, kuka ki shi, kuna cewa dubi mutum mai hadama, mai shan ruwan inabi da yawa, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!
35 Amma hikimar Allah tana shaidar dukan 'yayanta.”
36 Wata rana wani Bafarise, ya roki Yesu ya je ya ci abinci tare da shi. Bayan da Yesu ya shiga gidan Bafarisen, ya zauna a teburi domin ya ci abinci.
37 Sai ga wata mace mai zunubi, ta fito daga cikin birni. Sa'anda ta ji labari Yesu yana gidan Bafarisen, domin ya ci abinci. Ta dauki tandun mai na alabastar mai kamshi.
38 Ta tsaya kusa da Yesu tana kuka. Ta fara jika kafafunsa da hawayenta, tana shafe kafafunsa da gashin kanta. Tana yi wa kafafunsa sumba, tana shafe su da turare.
39 Sa'anda Bafarisen da ya gaiyaci Yesu, ya ga haka, sai ya yi tunani a cikin ransa, da cewa, “In da wannan mutum annabi ne, da ya gane ko wacce irin mace ce, wannan da take taba shi, ita mai zunubi ce.”
40 Yesu ya amsa ya ce masa, “Siman, ina so in gaya maka wani abu.” Ya ce, “malam sai ka fadi!”
41 Yesu ya ce, “wani mutum mai ba da bashi yana bin wadansu mutane su biyu kudi, yana bin dayan sule dari, dayan kuma yana bin sa sule hamsin.
42 Da yake ba su da kudin da za su iya biyan sa, sai ya yafe masu, su duka biyu. A cikin su biyu, wanne ne zai fi nuna kauna ga wannan mutum?”
43 Siman ya amsa ya ce, “Ina tsammani wanda ya yafe wa kudi da yawa.” Yesu ya amsa ya ce masa, “Ka shari'anta dai dai.”
44 Yesu ya juya wajen matar, ya ce da Siman, “Ka ga matan nan. Na shiga gidanka. Ba ka ba ni ruwa domin kafafuna ba, amma ita ta ba ni, da hawayenta ta wanke kafafuna, ta kuma shafe su da gashin kanta.
45 Kai ba ka yi ma ni sumba ba, amma ita ta yi, tun sa'adda na shigo nan ba ta dena sumbatar kafafuna ba.
46 Kai ba ka shafe kai na da mai ba, amma ita ta shafe kafafuna da turare.
47 Saboda haka, ita wadda ta ke da zunubi da yawa ta bayar da mai yawa, ta kuma nuna kauna mai yawa. Amma shi wanda aka gafarta wa kadan, ya kuma nuna kauna kadan.”
48 Daga nan sai ya ce mata, “An gafarta zunubanki.”
49 Wadanda su ke a nan zaune tare da shi suka fara magana da junansu, “Wanene wannan wanda har yake gafarta zunubai?
50 Sai Yesu ya ce da matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki tafi da salama.”