11
Da suka kusa Urushalima, kusa da Betafaji, da Betanya, wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu ya ce masu, “ ku shiga kauyen can kusa da mu. Da zarar kun shiga za ku ga aholaki a daure, wanda ba a taba hawa ba. Ku kwance shi, ku kawo mani. In wani ya ce maku, “Don me kuke haka? ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsa, zai kuma komo da shi nan da nan.”' Sai suka tafi, suka tadda aholakin a daure a kofar gida a bakin hanya, suka kwance shi. sai wadanda suke tsaye a gun suka ce masu, “Don me kuke kwance aholakin nan? Suka fada masu abinda Yesu yace, sai suka kyale su suka tafi. Almajiran nan biyu suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfida mayafansu a kai, sai ya hau. Sai mutane da yawa suka shimfida mayafansu a hanya, wadansu kuma suka baza ganyen da suka yanko daga filayen. Wadanda suke gaba da shi da wadanda ke bin bayansa suka yi sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji. 10 Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na Ubanmu Dawuda! Dukaka a cikin sama!” 11 San nan Yesu ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Sai ya dudduba komai, da magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyu nan. 12 Kashe gari, suka tashi daga Betanya, sai ya ji yunwa. 13 Da ya hango itacen baure mai ganye daga nesa sai ya je ya ga ko za sami 'ya'ya. Da ya iso wurinsa bai ga komai ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan baure ba ne. 14 Sai ya ce wa bauren, “Kada kowa ya kara cin ''ya'yanka har abada!” Almajiransa kuwa sun ji maganar. 15 Suka iso Urushalima, da shigar su, ya kori masu saye da sayarwa, ya watsar da taburan 'yan canjin kudi, da kujerun masu sayar da tantabaru. 16 Ya hana kowa ya dauki wani abu da za a i ya sayarwa a cikin haikalin. 17 Sai ya koyar da su cewa, “Ashe ba rubuce yake ba, “ Za a kira gidana gidan addu'a na dukan al'ummai? Amma ku kun mayar da shi kogon yan fashi”. 18 Da mayan Faristoci da marubutan attaura suka ji maganar da ya yi, sai suka nami hanyar da za su kashe shi. Amma suka ji tsoronsa domin dukkan taron na mamakin koyarwarsa. 19 Kowace yamma kuma, sukan fita gari. 20 Da safe suna wucewa, sai suka ga bauren nan ya bushe. 21 Bitrus kuwa ya tuna ya ce “Malam, dubi! Baurenan da ka la'anta ya bushe.” 22 Yesu ya amsa masu ya ce, “ ku gaskata da Allah.” 23 Hakika, ina gaya maku, duk wanda ya ce wa dutsen nan tashi ka fada cikin tekun', bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata haka kuwa zai faru, haka kuwa Allah zai yi. 24 Saboda haka ina dai gaya maku, komai kuka yi addu'a kuka roka, ku gaskata cewa samamme ne, zai kuma zama naku. 25 Duk sa'add da kuke addu'a ku gafarta wa wadanda suka yi maku laifi, domin Ubanku shima zai gafarta maku naku laifi.” 26 (Amma in baku gafartawa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma da ke sama ba zai gafarta maku ba.) 27 Da suka sake dawowa Urushalima. Yasu na tafiya cikin haikali, sai manyan firistoci, da marubuta, da dattawa suka zo wurinsa, 28 suka ce masa, “Da wanne iko kake yin wadanan abubuwa? Ko kuwa wa ya ba ka ikon yinsu? “ 29 Sai Yesu ya ce masu, “Zan yi maku wata tambaya. ku ba ni amsa, ni kuwa zan gaya maku ko da wanne iko ne nake yin wadannan abubuwan. 30 Baftismar da Yahaya yayi, daga sama take ko kuwa daga mutum take? ku bani amsa”. 31 Sai suka yi mahuwara da juna, suka ce, “in kuwa muka ce, 'daga sama take,' za ya ce, “To, don me ba ku gaskata shi ba? 32 In kuwa muka ce, “ amma in muka ce ta mutum ce zasu jejjefemu domi suna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne. 33 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba” Yesu ya ce masu, “Haka ni kuma ba zan fada muku ko da wanne iko nake yin abubuwan nan ba.”