3
Sai kuma ya sake tafiya cikin Majami'a sai ga wani Mutum mai shanyayyen hannu. Wadansu mutane suna kallonsa sosai, su gani ko zai warkar da shi a ranar Asabar. don su zarge shi. Yesu ya ce wa mai shanyayyen hanun “ Ka tashi ka tsaya a tsakiyar kowa.” Sai ya ce wa mutane, “Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta; a ceci rai, ko a yi kisa? “Amma suka yi shiru. Sai ya dube su cikin fushi, yana bakin ciki da taurin zuciyar su, ya ce wa mutumin ka mikar da hanunka, sai ya mikar da hanunsa Yesu kuwa ya warkar da shi. Sai Farisiyawa suka fita da sauri zuwa wurin mutanen Hirudus suka shirya yadda za su kashe shi. Sai Yesu da almajiransa, suka tafi bakin teku. sai mutane dayawa suka bi shi, daga Galili da Yahudiya Daga Urushalima da Edom gaba da Urdun da kewayan Taya da Sidon, da baban taro, ya ji abinda yake yi. suka zo wurinsa. Ya tambayi almajiransa su shirya masa karamin jirgin ruwa domin yawan mutane, domin kada su murkushe shi. 10 Ya warkar da mutane da yawa, yadda duk wadanda suke da cuttutuka suna kokari su taba shi. 11 Duk sa'adda kazaman ruhohin suka ganshi, sai su durkusa a gabansa su yi ihu da karfi su ce, kai Dan Allah ne.” 12 Ya umarce su da karfi kada su sa a san shi. 13 Ya hau saman dutsen, ya kira wadanda yake bukar su, su zo wurinsa. 14 Ya zabi guda goma sha biyu (ya kira su manzanni). Wadanda zasu kasance tare da shi, ya kuma aike su, su yi wa, azi, 15 Ya kuma basu Ikon fitar da aljanu. 16 Ya zabi guda goma sha biyu wato Saminu kuma yaba shi suna Bitrus. 17 Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan-uwan Yakubu wanda ya basu sunan Buwanarjis watau 'ya'yan tsawa, 18 da Andarawus da Filibus da Bartalamawus da Matta da Toma da Yakubu dan Halfa, da Taddawus da Saminu Ba-kananiye, 19 da Yahuza Iskariyoti wanda zai bashe shi. 20 Sa'adda ya shiga gida, Taron kuwa ya sake haduwa, har ya hana su cin abinci, 21 Da iyalansa suka ji haka, sai suka fito sun kamo shi, saboda sun ce, “Ai, baya cikin hankalinsa “ 22 Marubutan da suka zo daga Urushalima suka ce “Ai Ba'alzabuba ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.” 23 Yesu ya kirawo su wurinsa ya ce da su cikin misalai, “Yaya shaidan zai iya fitar da shaidan? 24 idan mulki ya rabu gida biyu ba zai tsayawa ba. 25 Haka in gida ya rabu kashi biyu, gaba da kansa bai zai tsaya ba. 26 Shaidan kuma in ya tayar wa kansa ya rabu, ba zai iya tsayawa ba, gama karshen sa ya zo kenan. 27 Amma ba mai iya shiga gidan kakkarfan mutum ya kwace kayansa, ba tare da ya fara daure kakkarfan mutumin ba, sa'an nan kuma ya kwashe kayan gidansa. 28 Hakika, ina gaya maku, dukan zunuban da mutane suka yi za a gafarta masu, da kowane irin sabon da suka furta, 29 amma fa duk wanda yayi sabon Ruhun Mai Tsarki baza a gafarta masa ba ko kadan, ya zama mai zunubi har abada.” 30 “Yesu ya fadi wadannan abubuwa domin suna cewa yana da ba kazamin ruhu,” 31 Sa'an nan uwatasa, da “Yan'uwansa suka zo suna tsaye a waje. sai suka aika masa, suna kuma umurtar sa ya zo. 32 Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka yi magana da shi da cewa, ga uwarka da yan-uwanka suna nan a waje, suna nemanka.” 33 Ya amsa masu, “Dacewa su wanene uwa-ta da “yan'uwa na? “ 34 Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, “Ga uwa-ta da yan-uwana anan! 35 Gama duk wanda ke yin abin da Allah yake so, shine dan'uwana da yar, uwata, da kuma uwa-ta.”