Wasikar Bulus Manzo Ta Fari Zuwa Ga Timoti
1
1 Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai cetonmu, da Almasihu Yesu begenmu,
2 zuwa ga Timoti, dana na gaske cikin bangaskiya: Alheri, jinkai da salama daga wurin Allah da Almasihu Yesu Ubangijinmu.
3 Kamar yadda na nanata maka ka yi, da zan tafi Makidoniya cewa, ka dakata a Afisa domin ka umarci wadansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam.
4 Kada su bata lokacinsu wajen sauraron tatsunniyoyi da kididdiga marar iyaka. Wannan yana haddasa gardandami, maimakon taimakawa shirin Allah, da ke ta wurin bangaskiya.
5 Manufar shari'a kuwa kauna ce daga tsabtacciyar zuciya, da tsatstsakan lamiri, da kuma sahihiyar bangaskiya.
6 Wadansu sun kauce daga tafarkin sun juya zuwa ga maganganun banza.
7 Suna so su zama malaman sha'ria, amma basu fahimci abin da suke fada ba ko abin da suka tsaya akai.
8 Amma mun sani shari'a tana da kyau idan an yi amfani da ita bisa ga ka'ida.
9 Gama mun san wannan, shari'a ba domin mai adalci take ba, amma domin marasa bin doka, mutane masu tawaye, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa Allah, da masu sabo. An bada shari'a domin masu kisan iyaye maza da iyaye mata, da masu kisan kai,
10 Domin fasikai da 'yan ludu, domin masu satar mutane su kai su bauta, domin makaryata, da masu shaidar zur, da kuma dukan abin da ke gaba da amintaccen umarni.
11 Wannan umarni bisa ga daukakkiyar bisharar Allah ne mai albarka, wadda aka bani amana.
12 Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijimu. wanda ya karfafa ni, gama ya karbe ni amintacce, ya sani cikin hidimarsa.
13 Dama can ni mai sabo ne, mai tsanantawa kuma dan ta'adda. Amma duk da haka aka yi mani jinkai domin na yi su cikin jahilci da rashin bangaskiya.
14 Amma alherin Ubangijinmu ya kwararo mani tare da bangaskiya, da kauna da ke cikin Almasihu Yesu.
15 Wannan bishara amintacciya ce, ta isa kowa ya karba, cewa Almasihu Yesu ya zo cikin duniya domin ceton masu zunubi, a cikinsu kuwa ni ne mafi lalacewa.
16 Saboda haka ne na sami jinkai, domin ta wurina ni na farko, a nuna hakurin Yesu Almasihu. Ya yi wannan domin in zama misali ga wadanda za su bada gaskiya zuwa rai madawwami.
17 Yanzu, ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, boyayye, Allah makadaici girma, da daukaka su tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.
18 Ina danka wannan umarni gareka, dana, Timoti. Ina haka ne bisa ga anabcin da aka yi a baya game da kai, domin ka shiga yaki mai kyau.
19 Ka yi wannan domin ka zama da bangaskiya da kyakkyawan lamiri. Wadansu mutane sun ki sauraron wannan suka yi barin bangaskiyarsu.
20 Kamar su Himinayus da Iskandari, wadanda na bada su ga shaidan domin su horu su koyi kin yi sabo.