14
A Ikoniyum
1 A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata. 2 Amma Yahudawan da suka ƙi ba da gaskata, suka zuga Al’ummai suka sa ɓata tsakaninsu da ’yan’uwa. 3 Bulus da Barnabas kuwa suka daɗe sosai a can, suna magana gabagadi saboda Ubangiji, wanda kuwa ya tabbatar da saƙon alherinsa ta wurinsa su su aikata ayyuka da alamu masu banmamaki. 4 Mutanen birnin suka rarrabu, waɗansu suka goyi bayan Yahudawa, waɗansu kuma suka goyi bayan manzannin. 5 Yahudawa da Al’ummai tare da shugabanninsu suka ƙulla shawara a tsakaninsu, domin su wulaƙanta su su kuma jajjefe su da duwatsu. 6 Amma suka sami labari suka kuma gudu zuwa biranen Ikoniyum na Listira da Derbe da kuma ƙauyukan kewaye, 7 inda suka ci gaba da wa’azin labari mai daɗi.
A Listira da Derbe
8 A Listira kuwa akwai wani gurgu zaune a ƙafafunsa, wanda gurgu ne tun haihuwa, kuma bai taɓa tafiya ba. 9 Ya kasa kunne yayinda Bulus yake magana. Bulus kuma ya kafa masa ido, ya lura cewa yana da bangaskiyar da za tă warkar da shi 10 sai ya ɗaga murya ya ce, “Tashi ka tsaya kan ƙafafunka!” Da jin haka, sai mutumin ya yi wuf ya kuma fara tafiya.
11 Sa’ad da taron suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka ihu da harshen Likayoniyawa, suna cewa, “Alloli sun sauka mana da siffar mutane!” 12 Sai suka ba wa Barnabas, sunan Zeyus, Bulus kuma suka kira Hermes domin shi ne shugaban magana. 13 Firist na Zeyus, wanda haikalinsa ke bayan birni, ya kawo bijimai da furanni a ƙofofin birni domin shi da taron mutanen sun so su miƙa musu hadayu.
14 Amma da manzannin nan Barnabas da Bulus suka ji haka, sai suka yayyage tufafinsu suka ruga cikin taron, suna ihu suna cewa, 15 “Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu. 16 A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama. 17 Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.” 18 Ko da waɗannan kalmomi ma, da ƙyar suka hana jama’an nan yin musu hadaya.
19 Sai waɗansu Yahudawa suka zo daga Antiyok da Ikoniyum suka sha kan taron. Suka jajjefi Bulus da duwatsu suka kuma ja shi bayan birni, suna tsammani ya mutu. 20 Amma bayan da almajiran suka taru kewaye da shi, sai ya tashi ya koma cikin birni. Kashegari shi da Barnabas suka tashi zuwa Derbe.
Komawa zuwa Antiyok a Suriya
21 Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok, 22 suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.” 23 Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa*Ko kuwa a Barnabas ya naɗa dattawa; ko kuwa Barnabas ya sa aka naɗa dattawa a kowace ikkilisiya, tare da addu’a da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi. 24 Bayan sun bi ta Fisidiya, sai suka zo cikin Famfiliya, 25 kuma sa’ad da suka yi wa’azi a Ferga, sai suka gangara zuwa Attaliya.
26 Daga Attaliya kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antiyok, inda dā aka danƙa su ga alherin Allah saboda aikin da suka kammala yanzu. 27 Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Al’ummai. 28 Suka kuma jima a can tare da almajirai.