15
Majalisa a Urushalima
Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.” Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana. Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Al’ummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan ’yan’uwa suka yi murna ƙwarai. Sa’ad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu.
Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”
Sai manzanni da dattawa suka taru don su duba maganar. Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata. Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu. Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya. 10 To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba? 11 A’a! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”
12 Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurinsu. 13 Da suka gama, sai Yaƙub ya yi magana ya ce, “’Yan’uwa, ku saurare ni. 14 Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Al’ummai su zama nasa. 15 Kalmomin annabawa sun yi daidai da wannan, kamar yadda yake a rubuce cewa,
16 “ ‘Bayan wannan zan koma
in kuma sāke gina tentin Dawuda da ya rushe.
Kufansa zan sāke gina,
in kuma mai da shi,
17 don ragowar mutane su nemi Ubangiji,
kuma duk Al’umman da suke kira bisa sunana,
in ji Ubangiji, wanda yake yin waɗannan abubuwa’*Amos 9.11,12
18 da aka sani tun zamanai.
19 “Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah. 20 A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini. 21 Gama Musa ya yi wa’azi a kowace birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majami’u kowane Asabbaci.”
Wasiƙar majalisa zuwa ga al’ummai masu bi
22 Sai manzanni da dattawa, tare da dukan ikkilisiya, suka yanke shawara su zaɓi waɗansu daga cikin mutanensu su kuma aike su zuwa Antiyok tare da Bulus da Barnabas. Sai suka zaɓi Yahuda (wanda ake kira Barsabbas) da kuma Sila, mutum biyu da suke shugabanni cikin ’yan’uwa. 23 Tare da su suka aika da wannan wasiƙa.
Daga manzanni da dattawa, ’yan’uwanku.
Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya.
Gaisuwa.
24 Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna tā da hankalinku ta wurin abin da suka ce. 25 Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus 26 mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi. 27 Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta. 28 Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa. 29 Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa.
Ku huta lafiya.
30 Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar. 31 Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa. 32 Yahuda da Sila, waɗanda su kansu annabawa ne, suka yi magana sosai don su gina su kuma ƙarfafa ’yan’uwa. 33 Bayan suka yi ’yan kwanaki a can, sai ’yan’uwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su.Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da su, 34 amma Sila ya yanke shawara ya dakata a can 35 Amma Bulus da Barnabas kuwa suka dakata a Antiyok, inda su da waɗansu da yawa suka yi koyarwa suka kuma yi wa’azin maganar Ubangiji.
Saɓani tsakanin Bulus da Barnabas
36 Bayan ’yan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci ’yan’uwa a duk garuruwan da muka yi wa’azin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.” 37 Barnabas ya so Yohanna, wanda ake kira Markus ya tafi tare da su, 38 amma Bulus bai ga ya kyautu ya tafi da shi ba, domin ya yashe su a Famfiliya bai kuwa ci gaba tare da su a aikin ba. 39 Suka sami saɓanin ra’ayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus, 40 amma Bulus ya zaɓi Sila suka kuwa tashi, bayan ’yan’uwa suka danƙa su ga alherin Ubangiji. 41 Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi.

*15:17 Amos 9.11,12

15:33 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da su, 34 amma Sila ya yanke shawara ya dakata a can