10
Mutane sun furta zunubansu
Yayinda Ezra yake addu’a, yake kuma furta laifi, yana kuka, yana a durƙushe da kansa ƙasa a gaban gidan Allah, sai babban taron jama’ar Isra’ilawa, maza, mata da yara, suka taru a wurinsa. Su ma suka yi kuka mai zafi. Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam ya ce wa Ezra, “Mun yi wa Allah rashin aminci ta wurin yin auratayya da maƙwabtanmu, amma duk da haka bai yashe mutanen Isra’ila ba. Yanzu bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori matan da yaransu bisa ga abin da ranka yă daɗe da sauran shugabannin da kuke girmama umarnin Allah kuka shawarce mu, bari mu yi haka bisa ga doka. Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, za mu ba ka goyon baya. Saboda haka ka yi ƙarfin hali ka aikata shi.”
Sai Ezra ya tashi ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra’ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar. Sa’an nan Ezra ya tashi daga gidan Allah ya tafi gidan Yehohanan ɗan Eliyashib, a can ma bai ci wani abu ba, bai sha ruwa ba domin ya ci gaba da yin baƙin cikin rashin aminci na waɗanda suka dawo daga bauta.
Aka yi shela a duk fāɗin Yahuda da Urushalima cewa dukan waɗanda suka dawo daga bauta su tattaru a Urushalima. Duk wanda bai zo a cikin kwana uku ba, za a washe shi, a kuma ware shi daga jama’ar da suka dawo daga bauta. Haka shugabanni da dattawa suka zartar.
 
A cikin kwana uku duk mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Urushalima. A ranar ashirin ga watan tara, dukan mutanen suka zauna a dandali a gaban gidan Allah cike da ɓacin rai saboda abin da ya faru da kuma ruwan da aka yi. 10 Sai Ezra firist ya miƙe tsaye ya yi musu magana ya ce, “Kun yi rashin aminci; kun aure mata baƙi, ta haka kuka ƙara kan zunubin Isra’ila. 11 Yanzu sai ku furta zunubanku ga Ubangiji, Allahn kakanninku, ku kuma yi nufinsa. Ku raba kanku da mutanen da suke kewaye da ku, ku kuma rabu da baƙin mata.”
12 Mutanen kuwa suka tā da murya da ƙarfi suka ce, “Gaskiya ka faɗa, dole mu yi yadda ka ce, 13 Amma akwai mutane da yawa, kuma lokacin damina ne; saboda haka ba za mu iya tsayawa a waje ba. Ban da haka ma, aikin nan ba na kwana ɗaya ko biyu ba ne, domin ba ƙaramin laifi muka yi ba. 14 Bari shugabanninmu su yi wani abu a madadin mutane duka, sa’an nan sai duk wanda ya san ya auri baƙuwar mace a garuruwanmu, sai yă zo nan a lokacin da aka shirya tare da dattawa da alƙalan kowane gari, har sai Allah ya huce fushinsa mai zafi da yake kanmu.” 15 Yonatan ɗan Asahel, da Yazehiya ɗan Tikba su ne kaɗai ba su yarda da wannan shirin ba, sai Meshullam da Shabbetai Balawe kuma suka goyi bayansu.
16 Sai waɗanda suka dawo daga bauta suka yi yadda aka zartar. Ezra firist ya zaɓi mutane waɗanda su ne shugabannin iyalai, ɗaya daga kowane sashe, aka rubuta sunan kowannensu. A ranar ɗaya ga watan goma kuwa suka zauna don su yi binciken waɗannan abubuwa. 17 A rana ta farko ga watan farko, suka gama da bincike duk waɗanda suka auri baƙin mata.
Masu laifin auratayya da baƙi
18 A cikin zuriyar firistoci, ga waɗanda suka auri mata baƙi.
Daga zuriyar Yeshuwa ɗan Yozadak da ’yan’uwansa, akwai Ma’asehiya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya. 19 (Su ne suka miƙa hannuwansu suka nuna sun yarda su kori matansu baƙi, kowannensu kuma ya ba da rago daga cikin garkensa don a miƙa hadaya don zunubi.)
20 Daga zuriyar Immer, akwai
Hanani da Zebadiya.
21 Daga zuriyar Harim, akwai
Ma’asehiya, Iliya, Shemahiya, Yehiyel da Uzziya.
22 Daga zuriyar Fashhur, akwai
Eliyohenai, Ma’asehiya, Ishmayel, Netanel, Yozabad da Eleyasa.
 
23 Cikin Lawiyawa, akwai
Yozabad, Shimeyi, Kelaya (wato, Kelita), Fetahahiya, Yahuda, Eliyezer.
24 Daga mawaƙa, akwai
Eliyashib.
Daga masu tsaron ƙofofin haikali, akwai
Shallum, Telem da Uri.
 
25 Ga sunayen sauran mutanen Isra’ilan da suke da wannan laifi.
Daga zuriyar Farosh, akwai
Ramiya, da Izziya, Malkiya, Miyamin, Eleyazar, Malkiya da Benahiya.
26 Daga zuriyar Elam, akwai
Mattaniya, Zakariya, Yehiyel, Abdi, Yeremot, da Iliya.
27 Daga iyalin Zattu, akwai
Eliyohenai, Eliyashib, Mattaniya Yeremot da Zabad da Aziza.
28 Daga zuriyar Bebai, akwai
Yehohanan, Hananiya, Zabbai, da Atlai.
29 Daga zuriyar Bani, akwai
Meshullam, Malluk, Adahiya, Yashub, Sheyal, da Ramot.
30 Daga zuriyar Fahat-Mowab, akwai
Adna, Kelal, Benahiya, Ma’asehiya, Mattaniya, Bezalel, Binnuyi, da Manasse.
31 Daga zuriyar Harim, akwai
Eliyezer, Isshiya, Malkiya, Shemahiya, Simeyon, 32 Benyamin, Malluk da Shemariya.
33 Daga zuriyar Hashum, akwai
Mattenai, da Mattatta, Zabad, Elifelet, Irmai, Manasse, da Shimeyi.
34 Daga zuriyar Bani, akwai
Ma’adai, Amram, Yuwel, 35 Benahiya, Bedeya, Keluhi, 36 Baniya, Meremot, Eliyashib, 37 Mattaniya, Mattenai da Ya’asu.
38 Daga zuriyar Binnuyi, akwai
Shimeyi, 39 Shelemiya, Natan, Adahiya, 40 Maknadebai, Shashai, Sharai, 41 Azarel, Shelemiya, da Shemariya, 42 Shallum da Amariya da Yusuf.
43 Daga zuriyar Nebo, akwai
Yehiyel, Mattitiya, Zabad, Zebina, Yaddai, Yowel da Benahiya.
 
44 Dukan waɗannan sun auri baƙin mata, waɗansunsu suna da ’ya’ya.