Nehemiya
1
Addu’ar Nehemiya
Kalmomin Nehemiya ɗan Hakaliya.
 
 
A cikin watan Kisleb a shekara ta ashirin, yayinda nake a fadar Shusha. Hanani, ɗaya daga cikin ’yan’uwana, ya zo daga Yahuda tare da waɗansu mutane. Na kuwa tambaye shi game da raguwar Yahudawan da suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta, da kuma game da Urushalima.
Suka ce mini, “Waɗanda suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta da kuma suka komo cikin yankin suna cikin babban damuwa da wulaƙanci. An rushe katangar Urushalima aka kuma ƙone ƙofofin da wuta.”
Da na ji waɗannan abubuwa, sai na zauna na yi kuka. Na yi kwanaki ina makoki da azumi, na kuma yi addu’a a gaban Allah na sama. Na ce,
“Ya Ubangiji Allah na sama, Allah mai girma da mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna da waɗanda suke ƙaunarsa, suke kuma yin biyayya da umarnansa, ka sa kunne ka kuma buɗe idanunka ka ji addu’ar da bawanka yake yi a gabanka dare da rana saboda bayinka, mutanen Isra’ila. Na furta zunuban da mu Isra’ilawa, har da ni da kuma gidan mahaifina muka yi maka. Mun yi mugunta gare ka. Ba mu yi biyayya da umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da ka ba wa bawanka Musa ba.
“Ka tuna da umarnan da ka ba wa bawanka Musa, kana cewa, ‘In kun yi rashin aminci, zan warwatsar da ku a cikin al’ummai, amma in kuka dawo gare ni kuka kuma yi biyayya da umarnaina, to, ko mutanenku da aka kwasa zuwa zaman bauta suna can wuri mafi nisa, zan tattara su daga can in kawo su wurin da na zaɓa yă zama wurin zama don Sunana.’
10 “Su bayinka ne da kuma mutanenka da ka fansa ta wurin ƙarfinka mai girma da kuma hannunka mai iko. 11 Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu’ar wannan bawanka da kuma ga addu’ar bayinka waɗanda suke farin cikin girmama sunanka. Ka ba wa bawanka nasara a yau ta wurinsa yă sami tagomashi a gaban wannan mutum.”
Ni ne mai riƙon kwaf sarki.