Habakkuk
1
1 Saƙon da annabi Habakkuk ya karɓa.
Habakkuk ya nuna damuwa
2 Har yaushe, ya Ubangiji, zan yi kukan neman taimako,
amma ka ƙi ji?
Ina kuka a gare ka saboda zalunci
amma ba ka ce ufam ba.
3 Me ya sa ka bari ina ta kallon rashin gaskiya?
Me ya sa kake barin abin da ba daidai ba?
Hallaka da tashin hankali suna a gabana;
ga rashin jituwa da faɗa ko’ina.
4 Saboda haka ba a bin doka,
shari’a kuma ba ta aiki.
Mugaye sun kewaye masu adalci
don a hana gaskiya tă yi aiki.
Amsar Ubangiji
5 “Ka dubi al’ummai, ka gani,
ka sha mamaki.
Ga shi zan yi wani abu a kwanakinka,
wanda ko ma an faɗa maka
ba za ka gaskata ba.
6 Zan tā da Babiloniyawa,*Ko kuwa Kaldiyawa
waɗannan marasa hankali da kuma marasa tausayi; masu gajeren haƙuri,
waɗanda suke ratsa ko’ina a duniya
don su ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.
7 Suna da bantsoro da firgitarwa;
dokoki da ƙa’idodinsu ne
kawai suka sani.
8 Dawakansu sun fi damisoshi sauri,
sun fi kyarketan yamma zafin rai.
Mahayansu suna zuwa a guje;
mahayansu daga nesa suka fito.
Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don yă ci mushe;
9 duk sukan zo da nufin tā-da-na-zaune-tsaye.
Ana jin tsoronsu tun ma kafin su iso
suna tattara bayi kamar yashi.
10 Sukan yi wa sarakuna ba’a
su kuma rena masu mulki.
Sukan yi wa dukan birane masu mafaka dariya;
sukan tara ƙasa su hau, su cinye abokan gābansu da yaƙi.
11 Sa’an nan su wuce da sauri kamar iska,
mutane ne masu laifi, waɗanda ƙarfinsu shi ne allahnsu.”
Damuwa ta biyu ta Habakkuk
12 Ya Ubangiji, ba tun fil azal kake ba?
Ya Allahna, Mai Tsarkina, ba za mu mutu ba.
Ya Ubangiji ka sanya su su tabbatar da hukunci;
Ya Dutse, ka naɗa su don su yi hukunci.
13 Idanunka masu tsarki ne da suka fi gaban duban mugunta;
ba ka amince da abin da ke ba daidai ba.
To, don me ka ƙyale munafukai suna cin karensu ba babbaka?
Me ya sa kake shiru sa’ad da mugaye
suke haɗiye adalai da suka fi su adalci?
14 Ka mai da maza kamar kifin teku,
kamar halittun tekun da ba su da shugaba.
15 Mugu abokin gāba yakan kama su duka da ƙugiya,
yă jawo su waje da abin kamun kifinsa,
yă tattara su cikin ragarsa,
ta haka yakan yi murna da farin ciki.
16 Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa
yă kuma ƙona turare wa ragarsa,
domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi
yă kuma zaɓi irin abincin da yake so.
17 Zai ci gaba da juye abin kamun kifinsu ke nan,
suna hallaka al’ummai ba tausayi?