3
Kaiton Ninebe
Kaiton birni mai zub da jini,
wadda take cike da ƙarairayi,
cike da ganima,
wadda ba a rasa masu fāɗawa cikin wahala!
Ku ji karar bulala
da kwaramniyar ƙafafu,
da sukuwar dawakai
da girgizar kekunan yaƙi!
Mahaya dawakai sun kunno kai,
takuba suna walƙiya,
māsu kuma suna ƙyali;
ga ɗumbun da aka kashe
ga tsibin matattu,
gawawwaki ba iyaka,
mutane suna tuntuɓe da gawawwaki,
duk saboda yawan sha’awace-sha’awacen karuwa,
mai daɗin baki, uwargidan maita,
wadda ta ɓad da al’ummai ta wurin karuwancinta
ta kuma ɓad da mutane ta wurin maitancinta.
 
“Ina gāba da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Zan kware fatarinki a idonki.
Zan nuna wa al’ummai tsiraicinki,
masarautai kuma kunyarki.
Zan watsa miki ƙazanta,
in yi miki wulaƙanci
in kuma mai da ke abin reni.
Duk wanda ya gan ki zai gudu daga gare ki yana cewa,
‘Ninebe ta lalace, wa zai yi makoki domin ta?’
Ina zan sami wani wanda zai yi miki ta’aziyya?”
 
Kin fi Tebes*Ibraniyanci Ba Amon ne
da take a bakin Nilu,
da ruwa yake kewaye da ita?
Rafi shi ne kāriyarta,
ruwanta kuma katanga.
KushWato, yankin Nilu na Bisa da kuma Masar su ne ƙarfinta marar iyaka;
Fut da Libiya suna cikin mataimakanta.
10 Duk da haka an tafi da ita
ta kuma tafi bauta.
Aka fyaɗa ƙanananta da ƙasa
aka yayyanka su gunduwa-gunduwa a kan kowane titi.
Aka jefa ƙuri’a a kan manyan mutanenta,
aka daure manyan mutanenta da sarƙoƙi.
11 Ke ma za ki bugu,
za ki ɓuya.
Ki kuma nemi mafaka daga wurin abokin gāba.
 
12 Dukan kagarunki suna kama da itatuwan ɓaure
da ’ya’yansu da suka nuna.
Da an girgiza,
sai ɓaure su zuba a bakin mai sha.
13 Dubi mayaƙanki,
duk mata ne!
Ƙofofin ƙasarki
a buɗe suke ga abokan gābanki,
wuta ta cinye madogaransu.
 
14 Ki ja ruwa gama za a kewaye ki da yaƙi.
Ki ƙara ƙarfin kagaranki!
Ki kwaɓa laka,
ki sassaƙa turmi
ki gyara abin yin tubali!
15 A can wuta za tă cinye ki;
takobi zai sare ki,
kuma kamar fāra, za a cinye ki.
Ki riɓaɓɓanya kamar fāra,
ki riɓaɓɓanya kamar fārin ɗango!
16 Kin ƙara yawan masu kasuwancinki
har sai da suka fi taurarin sama.
Amma kamar fāra sun cinye ƙasar
sa’an nan suka tashi, suka tafi.
17 Masu tsaronki suna kama da fāri ɗango,
shugabanninki sun yi cincirindo kamar fārin ɗango
da suka sauka a kan bango a rana mai sanyi,
amma da rana ta fito, duk za su tashi su tafi,
ba kuma wanda ya san inda suka nufa.
 
18 Ya sarkin Assuriya, makiyayankaKo kuwa masu mulki sun yi barci;
manyan mutanenka sun kwanta su huta.
An watsar da mutanenka a cikin duwatsu,
ba wanda zai tattaro su.
19 Ba abin da zai warkar da rauninka;
rauninka ya yi muni.
Duk wanda ya ji labarinka
zai tafa hannuwansa saboda farin cikin fāɗuwarka,
gama wane ne bai ji
jiki a hannunka ba?

*3:8 Ibraniyanci Ba Amon

3:9 Wato, yankin Nilu na Bisa

3:18 Ko kuwa masu mulki