25
Yabo ga Ubangiji
1 Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,
gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,
abubuwan da aka shirya tun da.
2 Ka mai da birnin tsibin tarkace,
ka lalatar da gari mai katanga,
birnin baƙi mai ƙarfi, ta ɓace; ba za a ƙara gina ta ba.
3 Saboda haka mutane masu ƙarfi za su girmama ka;
biranen mugayen al’ummai za su ji tsoronka.
4 Kai ka zama mafakar matalauta, mafaka don mabukata cikin damuwa,
wurin ɓuya daga hadari, inuwa kuma daga zafin rana.
Gama numfashin mugaye yana kamar da hadari mai bugun bango
5 kuma kamar zafin hamada.
Ka kwantar da hayaniyar baƙi;
kamar yadda inuwar girgije kan rage zafin rana, haka ake kwantar da waƙar mugaye.
6 A kan wannan dutse Ubangiji Maɗaukaki zai shirya bikin abinci mai kyau don dukan mutane,
liyafar ajiyayyen ruwan inabi da nama mafi kyau da ruwan inabi mafi kyau.
7 A wannan dutse zai kawar da
baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane,
ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai;
8 zai haɗiye mutuwa har abada.
Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye
daga dukan fuskoki;
zai kawar da kunyar mutanensa
daga dukan duniya.
Ubangiji ne ya faɗa.
9 A wannan rana za su ce,
“Tabbatacce wannan shi ne Allah;
mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu.
Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi;
bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”
10 Hannun Ubangiji zai zauna a kan wannan dutse;
amma za a tattake Mowab a ƙarƙashinsa
kamar yadda ake tattaka kara a cikin taki.
11 Za su buɗe hannuwansa a cikinsa,
yadda mai iyo kan buɗe hannuwansa don yă yi iyo.
Allah ya ƙasƙantar da girmankansu
duk da wayon*Ma’anar kalmar Ibraniyancin nan babu tabbas. hannuwansu.
12 Zai rurrushe manyan katangar kagaru
ya kuma ƙasƙantar da su;
zai rushe su har ƙasa,
su zama ƙura.