66
Hukunci da kuma bege
1 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Sama kursiyina ce,
duniya kuma matashin sawuna.
Ina gidan da za ku gina mini?
Ina wurin hutuna zai kasance?
2 Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa,
ta haka suka kasance?”
In ji Ubangiji.
“Wannan mutum ne nake jin daɗi,
shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba,
yana kuma rawar jiki ga maganata.
3 Amma duk ya miƙa hadayar bijimi
yana kama da wanda ya kashe mutum,
kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago,
kamar wanda ya karye wuyan kare;
duk wanda ya miƙa hadaya ta gari
yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade,
kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni,
kamar wanda yake bauta gunki ne.
Sun zaɓi hanyoyinsu,
rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;
4 saboda haka ni ma zan aukar musu da masifa mai zafi
in kuma kawo musu abin da suke tsoro.
Gama sa’ad da na yi kira, ba wanda ya amsa,
sa’ad da na yi magana, ba wanda ya saurara,
Sun aikata mugunta a idona
suka kuma zaɓa abin da ba na jin daɗi.”
5 Ku ji maganar Ubangiji,
ku da kuke rawar jiki ga maganarsa,
“’Yan’uwanku da suke ƙinku,
suna kuma ware ku saboda sunana, sun ce,
‘Bari a ɗaukaka Ubangiji,
don mu ga farin cikinku!’
Duk da haka za su sha kunya.
6 Ku ji wannan hayaniya daga birni,
ku ji surutu daga haikali!
Amon Ubangiji ne
yana sāka wa abokan gābansa abin da ya dace da su.
7 “Kafin naƙuda ya fara mata,
ta haihu;
kafin zafi ya zo mata,
ta haifi ɗa.
8 Wa ya taɓa jin irin wannan abu?
Wa ya taɓa gani irin abubuwan nan?
Za a iya ƙirƙiro ƙasa a rana ɗaya
ko a haifi al’umma farat ɗaya?
Duk da haka da zarar Sihiyona ta fara naƙuda
sai ta haifi ’ya’yanta.
9 Zan kai mace har haihuwa
in kuma sa ta kāsa haihu?” In ji Ubangiji.
“Zan rufe mahaihuwa
sa’ad da lokacin haihuwa ya yi?” In ji Allahnku.
10 “Ku yi farin ciki tare da Urushalima ku kuma yi murna saboda ita,
dukanku waɗanda kuke ƙaunarta;
ku yi farin ciki matuƙa tare da ita,
dukanku waɗanda kuke makoki a kanta.
11 Gama za ku tsotsa ku kuma ƙoshi
da nonon ta’aziyyarta;
za ku sha sosai
ku kuma ji daɗin yalwarta.”
12 Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa,
“Zan fadada salama gare ta kamar kogi,
wadatar al’ummai kuma kamar rafi mai gudu;
za ku tsotsa a kuma riƙe ku a hannunta
ku kuma yi wasa a gwiwoyinta.
13 Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta
haka zan ta’azantar da ku;
za ku kuma ta’azantu a Urushalima.”
14 Sa’ad da kuka ga wannan, zuciyarku za tă yi farin ciki
za ku kuma haɓaka kamar ciyawa;
za a sanar da hannun Ubangiji ga bayinsa,
amma za a nuna wa maƙiyansa fushinsa.
15 Ga shi, Ubangiji yana zuwa da wuta,
kuma kekunan yaƙinsa suna kama da guguwa;
zai sauko da fushinsa da zafi,
tsawatawarsa kuma da harsunan wuta.
16 Gama da wuta da kuma takobi
Ubangiji zai yi hukunci a kan dukan mutane,
kuma yawanci za su kasance waɗanda Ubangiji zai kashe.
17 “Waɗanda suka tsarkake suka kuma tsabtacce kansu don su je lambu, suna bin wannan da yake tsakiya*Ko kuwa lambu a bayan wannan na masujadanku, kuma waɗannan da suke cin naman aladu da ɓeraye da waɗansu abubuwan banƙyama, za su sadu da ƙarshensu tare,” in ji Ubangiji.
18 “Ni kuwa, saboda ayyukansu da kuma tunaninsu, ina dab da zuwa in tattara dukan al’ummai da harsuna, za su kuma zo su ga ɗaukakata.
19 “Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun ’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai. 20 Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore. 21 Zan kuwa zaɓa waɗansunsu kuma su zama firistoci da Lawiyawa,” in ji Ubangiji.
22 “Kamar yadda sabuwar duniya da sabuwar sama za su tabbata a gabana,” in ji Ubangiji, “haka sunanku da zuriyarku za su tabbata. 23 Daga wannan sabon wata zuwa wancan, kuma daga wannan Asabbaci zuwa wancan, dukan mutane za su zo su rusuna a gabana,” in ji Ubangiji. 24 “Za su kuma fita su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa; tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, balle wutar da take ƙona su ta mutu, za su kuma zama abin ƙyama ga dukan mutane.”