Irmiya
1
Kalmomin Irmiya ɗan Hilkiya, ɗaya daga cikin firistoci a Anatot a yankin Benyamin. Maganar Ubangiji ta zo gare shi a shekara ta goma sha uku ta sarautar Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda, da kuma a zamanin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, har zuwa watan biyar na shekara goma sha ɗaya na Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, sa’ad da aka kai mutanen Urushalima zaman bauta.
 
Kiran Irmiya
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
“Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san* Ko kuwa zaɓe ka,
kafin a haife ka, na keɓe ka;
na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.”
Sai na ce, “Kayya, Ubangiji Mai Iko Duka, ban iya magana ba; ni ɗan yaro ne kawai.”
Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka,” in ji Ubangiji.
Sai Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina ya ce mini, “Yanzu na sa kalmomina a bakinka. 10 Duba, yau na naɗa ka a kan al’ummai da mulkoki don ka tumɓuke ka kuma rusar, ka hallaka ka kuma kakkaɓe, ka gina ka kuma shuka.”
11 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Me ka gani, Irmiya?”
Sai na amsa na ce, “Na ga reshen itacen almon.”
12  Ubangiji ya ce mini, “Daidai ne ka gani, gama ina lura in ga cewa maganata ta cika.”
13 Maganar Ubangiji ta sāke zo mini cewa, “Me ka gani?”
Na amsa na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, tana juyewa daga arewa.”
14  Ubangiji ya ce mini, “Daga arewa za a zubo masifa a kan dukan mazaunan ƙasar. 15 Ina shirin kiran dukan mutanen masarautar arewanci,” in ji Ubangiji.
“Sarakunansu za su zo su kafa kursiyoyinsu
a mashigin ƙofofin Urushalima;
za su zo su kewaye dukan katangarta
su kewaye dukan garuruwan Yahuda.
16 Zan furta hukunci a kan mutanena
saboda muguntarsu na yashe ni,
suna ƙona turare ga waɗansu alloli
suna kuma bauta wa abin da hannuwansu suka yi.
17 “Ka kintsa kanka! Ka tashi tsaye ka faɗa musu abin da na umarce ka. Kada su firgita ka, in ba haka ba zan firgita ka a gabansu. 18 Yau na mai da kai birni mai katanga, ginshiƙin ƙarfe da bangon tagulla don ka tsaya gāba da dukan ƙasar, ya kuma yi gāba da sarakunan Yahuda da fadawan, da firistoci da kuma mutanenta. 19 Za su yi yaƙi da kai amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, zan kuma kiyaye ka,” in ji Ubangiji.

*1:5 Ko kuwa zaɓe