Yunana
1
Yunana ya gudu daga Ubangiji
Maganar Ubangiji ta zo wa Yunana ɗan Amittai cewa, “Tafi babban birnin nan Ninebe ka yi mata wa’azi, saboda muguntarta ta haura zuwa gabana.”
Amma Yunana ya gudu daga Ubangiji ya nufi Tarshish. Ya gangara zuwa Yaffa, inda ya sami jirgin ruwa mai shirin tashi daga tashar. Bayan ya biya kuɗin tafiya, sai ya shiga jirgi ya kama hanya zuwa Tarshish don yă tsere wa Ubangiji.
Sai Ubangiji ya aika da babban iska a bisan teku, hadiri ya tsananta ƙwarai har jirgin ya yi barazanar farfashewa. Dukan matuƙan jirgin suka tsorata, kowannensu kuma ya yi kuka ga allahnsa, suka kuma jefar da kayan jirgi a cikin teku domin su rage nauyin jirgin.
Ana cikin haka, ashe, Yunana ya sauka can ƙarƙashin jirgi ya je ya kwanta, yana ta sharar barcinsa. Sai kyaftin ɗin ya je wajensa ya ce masa, “Don me kake barci? Tashi ka kira bisa ga allahnka! Mai yiwuwa yă ji mu, yă cece mu don kada mu hallaka.”
Matuƙan jirgin suka ce wa juna, “Ku zo, mu jefa ƙuri’a mu ga wa ke da alhakin wannan masifa.” Sai suka jefa ƙuri’a, ƙuri’ar kuwa ta fāɗa a kan Yunana. Saboda haka suka tambaye shi suka ce, “Yanzu, gaya mana, dalilin da ya sa wannan masifa ta zo mana? Mene ne aikinka? Daga ina ka fito? Ina ne ƙasarka? Daga wacce kabila ce ka fito?”
Sai ya amsa, “Ni mutumin Ibraniyawa ne, ina kuma bauta wa Ubangiji Allah na sama, wanda ya yi teku da tuddai.”
10 Sai matuƙan jirgin suka tsorata ƙwarai, suka ce masa, “Wane irin mugun abu ne ka aikata haka?” (Sun gane cewa yana gudu ne daga wurin Ubangiji, domin ya riga ya faɗa musu.)
11 Sai tekun ya daɗa rikicewa. Sai suka tambaye shi, “Me za mu yi da kai domin tekun yă daina hauka?”
12 Ya amsa musu ya ce, “Ku ɗauke ni ku jefa a cikin teku, tekun zai kwanta. Na san cewa laifina ne ya jawo wannan babban hadirin da ya auka muku.”
13 Maimakon mutanen su yi haka, sai suka yi ƙoƙari su tura jirgin ruwan zuwa bakin teku. Amma ba su iya ba, saboda iskar ta sa tekun ya yi ta ƙara hauka. 14 Sai suka yi kuka ga Ubangiji suka ce, “Ya Ubangiji, in ka yarda kada ka bar mu mu mutu saboda ran mutumin nan. Kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka ga ya gamshe ka.” 15 Sa’an nan suka ɗauki Yunana suka jefar da shi daga jirgin, sai tekun ya kwanta. 16 Ganin haka sai mutanen suka cika da tsoron Ubangiji, suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya, suka yi wa’adi da shi.
Addu’ar Yunana
17 Amma Ubangiji ya tanada wani babban kifi da zai haɗiye Yunana, Yunana kuwa ya yi yini uku da dare uku a ciki cikin kifin.