Obadiya
1
Wahayin Obadiya.
 
 
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce a kan Edom.
Mun ji saƙo daga wurin Ubangiji cewa,
An aiki jakada zuwa ga al’ummai yă faɗa musu cewa,
“Ku tashi, mu tafi mu yi yaƙi da ita.”
 
“Duba, zan maishe ki ƙarama a cikin al’ummai;
za a rena ki ƙwarai.
Fariyar zuciyarki ta yaudare ki,
ke da kike zama can bisa duwatsu* Ko kuwa na Sela
kika kuma yi gidanki a kan ƙwanƙoli,
ke da kike ce wa kanki,
‘Wa zai iya saukar da ni ƙasa?’
Ko da yake kina firiya kamar gaggafa
kin kuma yi sheƙarki a can cikin taurari,
daga can zan saukar da ke,”
in ji Ubangiji.
“In ɓarayi suka zo miki,
in kuma ’yan fashi suka shigo gidan da dare,
kash, bala’i zai jira ki
ba abin da suke so ne kawai za su sata ba?
In kuma masu tsinka ’ya’yan inabi suka zo miki,
ba sukan bar ’ya’yan inabi kaɗan ba?
Amma za a washe Isuwa ƙaƙaf,
a kuma yaye ɓoyayyiyar dukiyarsa!
Dukan waɗanda kike tarayya da su, za su kore ki zuwa iyaka;
abokanki kuma za su yaudare ki, su kuma sha ƙarfinki;
waɗanda suke cin abincinki, za su sa miki tarko, Ma’anar Ibraniyanci don wannan babu tabbas.
amma ba za ki gane ba.
 
“A wannan rana,” in jin Ubangiji,
“zan hallaka masu hikimar Edom,
zan shafe mutane masu fahima a duwatsun Isuwa.
Jarumawanki, ya Teman, za su razana,
za a kashe kowane mutum a duwatsun Isuwa.
10 Saboda halin kama-karyar da kika yi wa ɗan’uwanka Yaƙub,
za ki sha kunya;
za a hallaka ki har abada.
11 A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido
yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki,
baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa
suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima,
kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa.
12 Bai kamata ki rena ɗan’uwanki
a ranar masifarsa ba,
ko ki yi farin ciki a kan mutanen Yahuda
a ranar hallakarsu,
ko ki yi fariya sosai
a ranar wahalarsu.
13 Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena
a ranar bala’insu ba,
ko ki rena su a cikin masifarsu
a ranar bala’insu,
ko ki ƙwace dukiyarsu
a ranar bala’insu ba.
14 Bai kamata ki tsaya a mararraba
don ki kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa ba,
ko ki ba da waɗanda suka tsere ga hannun maƙiyansu
a ranar wahalarsu ba.
 
15 “Ranar Ubangiji ta yi kusa
don dukan al’ummai.
Kamar yadda kuka yi, haka za a yi muku;
ayyukanku za su koma a kanku.
16 Kamar yadda kuka sha a kan tuduna mai tsarki,
haka dukan al’ummai za su yi ta sha,
za su sha, su kuma sha
su zama sai ka ce ba su taɓa kasancewa ba.
17 Amma a kan Dutsen Sihiyona za a sami ceto;
Dutsen zai zama mai tsarki,
gidan Yaƙub kuma
zai mallaki gādonsa.
18 Gidan Yaƙub zai zama kamar wuta,
gidan Yusuf kuma kamar harshen wuta;
gidan Isuwa zai zama kamar tattaka,
za a kuma sa masa wuta yă ƙone.
Babu wanda zai tsira
daga gidan Isuwa.”
Ni Ubangiji na faɗa.
 
19 Mutane daga Negeb za su mamaye
duwatsun Isuwa,
mutane kuma daga gindin tuddai za su mallaki
ƙasar Filistiyawa.
Za su mamaye filayen Efraim da Samariya,
Benyamin kuwa zai mallaki Gileyad.
20 Wannan ƙungiyar Isra’ilawan da aka kwashe zuwa bauta da suke a Kan’ana
za su mallaki ƙasar har zuwa Zarefat;
waɗannan da aka kwashe zuwa bauta daga Urushalima da suke a Sefarad
za su mallaki garuruwan Negeb.
21 Masu kawo ceto za su haura zuwa Ko kuwa daga Dutsen Sihiyona
don su yi mulkin duwatsun Isuwa.
Ubangiji ne zai yi mulki.

*1:3 Ko kuwa na Sela

1:7 Ma’anar Ibraniyanci don wannan babu tabbas.

1:21 Ko kuwa daga