9
Isra’ilawa sun furta zunubansu
A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, Isra’ilawa suka taru, suna yin azumi, suna sa rigunan makoki, suna kuma zuba toka a kansu. Waɗanda suke zuriyar Isra’ilawa suka ware kansu daga dukan baƙi. Suka tsaya, suka kuma furta zunubansu da muguntar kakanninsu. Sa’ad da suke nan a tsaye, aka ɗauki awa uku ana karanta Littafin Dokar Ubangiji Allahnsu. Aka kuma ɗauki awa uku ana sujada ga Ubangiji Allahnsu. A kan dakalin kuwa akwai Lawiyawa, wato, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani da Kenani tsaye, waɗanda suka kira da babbar murya ga Ubangiji Allahnsu. Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, “Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin.”
“Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo. Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.
“Kai ne Ubangiji Allah, wanda ya zaɓi Abram, ya fitar da shi daga Ur na Kaldiyawa, ya kuma ba shi suna Ibrahim. Kai ka sami zuciyarsa da aminci a gare ka, ka kuma yi alkawari da shi cewa za ka ba zuriyarsa ƙasar Kan’aniyawa, da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, da ta Yebusiyawa, da kuma ta Girgashiyawa. Ka kiyaye alkawarinka domin kai mai adalci ne.
“Ka ga wahalar kakanninmu a Masar; ka kuwa ji kukansu a Jan Teku. 10 Ka aika da alamu masu banmamaki da al’ajabai a kan Fir’auna, a kan dukan shugabanninsa da kuma a kan dukan mutanen ƙasarsa, gama ka ga irin danniyar da suka yi wa mutanenka. Ka samo wa kanka suna, wadda ta dawwama har yă zuwa yau. 11 Ka raba teku a gaban kakanninmu, saboda su wuce cikinsa a busasshiyar ƙasa, amma ka hallaka masu binsu cikin zurfafa, nutse kamar dutse a cikin ruwa. 12 Da rana ka bishe kakanninmu da girgije, da dare kuwa ka bishe su da ginshiƙin wuta don ka ba su haske a hanyar da za su bi.
13 “Ka sauko a kan Dutsen Sinai; ka yi musu magana daga sama. Ka ba su ƙa’idodi da dokokin da suke masu adalci da kuma daidai, ka ba su farillai da umarnai da suke da kyau. 14 Ka sanar da su Asabbacinka mai tsarki, ka kuma ba su umarnai, da farillai, da kuma dokoki ta wurin bawanka Musa. 15 Cikin yunwansu ka ba su burodi daga sama, cikin ƙishirwansu kuma ka fitar musu ruwa daga dutse. Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka rantse ta wurin ɗaga hannu cewa za ka ba su.
16 “Amma su kakanninmu, suka yi fariya da taurinkai, ba su kuwa yi biyayya ga umarnanka ba. 17 Suka ƙi su saurare ka, suka kāsa tuna da mu’ujizan da ka aikata a cikinsu. Suka yi taurinkai, cikin tawayensu kuma suka naɗa shugaba don su koma bautarsu. Amma kai Allah ne mai gafartawa, mai alheri da jinƙai, mai jinkirin fushi, mai yalwar ƙauna. Saboda haka ba ka yashe su ba, 18 ko ma sa’ad da suka yi wa kansu siffar ɗan maraƙi, suka ce, ‘Wannan shi ne allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar,’ ko sa’ad da suka yi saɓo mai bantsoro.
19 “Saboda jinƙanka mai girma, ba ka yashe su a hamada ba. Da rana, ginshiƙin girgije bai daina bishe su a hanyarsu ba, da dare kuma ginshiƙin wuta bai daina haskakawa a hanyar da za su bi ba. 20 Ka ba da Ruhunka mai kyau don yă koyar da su. Ba ka janye Manna naka daga bakunansu ba, ka kuma ba su ruwa don ƙishirwansu. 21 Shekaru arba’in ka riƙe su a cikin hamada; ba su rasa kome ba, rigunansu ba su yage ba, ƙafafunsu kuwa ba su kumbura ba.
22 “Ka ba su mulkoki da al’ummai, kana ba su har ma da ƙasashen da suke jeji. Suka ci ƙasar Sihon na sarkin Heshbon da ƙasar Og inda sarkin Bashan yake mulki. 23 Ka sa ’ya’yansu maza suka yi yawa kamar taurarin sararin sama, ka kuma kawo su cikin ƙasar da ka faɗa wa kakanninsu su shiga su mallake. 24 ’Ya’yansu maza suka shiga suka kuma mallaki ƙasar. A gabansu ka rinjayi Kan’aniyawan da suke zama a cikin ƙasar; ka ba da Kan’aniyawa a gare su, tare da sarakunansu da kuma mutanen ƙasar, su yi da su yadda suke so. 25 Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma.
26 “Amma suka yi rashin biyayya suka kuma yi tawaye gare ka; suka sa dokarka a bayansu. Suka kashe annabawanka waɗanda suka gargaɗe su don su mai da su gare ka; suka aikata saɓo mai bantsoro. 27 Saboda haka ka miƙa su ga abokan gābansu waɗanda suka yi musu danniya. Amma sa’ad da ake danniyarsu sai suka yi kuka gare ka. Daga sama ka ji su, cikin jinƙanka mai girma kuwa ka ba su mai ceto, wanda ya fisshe su daga hannun abokan gābansu.
28 “Amma nan da nan, da suka sami hutu, sai suka sāke aikata abin da yake mugu a idonka. Sai ka yashe su ga hannun abokan gābansu don su yi mulki a kansu. Sa’ad da suka yi kuka kuma gare ka, ka ji daga sama, cikin jinƙanka kuma ka fisshe su sau da sau.
29 “Ka gargaɗe su su dawo ga dokarka, amma suka yi fariya, suka bijire wa umarnanka. Suka yi zunubi game da farillanka waɗanda ta wurinsu ne mutum zai rayu in ya yi biyayya da su. Cikin taurinkai suka juye bayansu daga gare ka, suka zama masu taurinkai, suka kuma ƙi su saurara. 30 Shekaru masu yawa ka yi haƙuri da su. Ta wurin Ruhunka ka gargaɗe su ta wurin annabawa. Duk da haka ba su kasa kunne ba, saboda haka ka miƙa su ga maƙwabtansu. 31 Amma cikin tausayinka mai girma ba ka kawo su ga ƙarshe ko ka yashe su ba, gama kai Allah ne mai alheri da kuma mai jinƙai.
32 “To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau. 33 Cikin dukan abubuwan da suka faru da mu, ka kasance mai adalci; ka yi aminci, yayinda mu kuwa muka aikata mugu. 34 Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu da kuma kakanninmu ba su bi dokarka ba, ba su ma mai da hankali ga umarnanka ko gargaɗin da ka yi musu ba. 35 Ko ma yayinda suke a masarautarsu, suna jin daɗin girmar kyautatawarka gare su, cikin ƙasar mai girma, da kuma mai fāɗin da ka ba su, ba su bauta maka ko su juye daga mugayen hanyoyinsu ba.
36 “Amma duba, mu bayi ne a yau, bayi a ƙasar da ka ba kakanninmu don su ci amfaninta da kuma waɗansu abubuwa masu kyau da take bayarwa. 37 Saboda zunubanmu, yalwar girbin da muke samu yana tafiya wurin sarakunan da ka sa a kanmu. Suna mulki bisa jikunanmu, da bisa garkenmu yadda suka ga dama. Muna cikin baƙin ciki.
Alkawarin mutane
38 “Saboda wannan duka, muna yin zaunannen alkawari, muna sa shi a rubuce, shugabanninmu kuwa da Lawiyawanmu, da firistocinmu suna buga hatimansu a kai.”