10
1 Waɗanda suka buga hatimin su ne,
Nehemiya ɗan Hakaliya, wanda yake gwamna.
Zedekiya 2 da Serahiya, da Azariya, da Irmiya,
3 da Fashhur, da Amariya, da Malkiya,
4 da Hattush, da Shebaniya, da Malluk,
5 da Harim, da Meremot, da Obadiya,
6 da Daniyel, da Ginneton, da Baruk,
7 da Meshullam, da Abiya, da Miyamin,
8 da Ma’aziya, da Bilgai, da kuma Shemahiya.
Waɗannan su ne Firistocin.
9 Lawiyawan kuwa su ne,
Yeshuwa ɗan Azaniya, da Binnuyi ɗan Henadad, da Kadmiyel,
10 ’yan’uwansu kuwa su ne, Shebaniya,
da Hodiya, da Kelita, da Felahiya, da Hanan,
11 da Mika, da Rehob, da Hashabiya,
12 da Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya,
13 da Hodiya, da Bani da kuma Beninu.
14 Shugabannin mutane su ne,
Farosh, da Fahat-Mowab, da Elam, da Zattu, da Bani,
15 da Bunni, da Azgad, da Bebai,
16 da Adoniya, da Bigwai, da Adin,
17 da Ater, da Hezekiya, da Azzur,
18 da Hodiya, da Hashum, da Bezai,
19 da Harif, da Anatot, da Nebai,
20 da Magfiyash, da Meshullam, da Hezir,
21 da Meshezabel, da Zadok, da Yadduwa
22 da Felatiya, da Hanan, da Anahiya,
23 da Hosheya, da Hananiya, da Hasshub,
24 da Hallohesh, da Filha, da Shobek,
25 da Rehum, da Hashabna, da Ma’asehiya
26 da Ahiya, da Hanan, da Anan,
27 da Malluk, da Harim da kuma Ba’ana.
28 “Sauran mutane, wato, firistoci, Lawiyawa, matsaran ƙofofi, mawaƙa, ma’aikatan haikali da dukan waɗanda suka ware kansu daga maƙwabta saboda Dokar Allah, tare da matansu da dukan ’ya’yansu maza da mata waɗanda za su iya fahimta, 29 dukan waɗannan yanzu suka sadu da manyan gari ’yan’uwansu, suka rantse, cewa la’ana ta same su idan ba su kiyaye Dokar Allah da aka bayar ta wurin Musa bawan Allah su kuma mai da hankali ga yin biyayya da dukan umarnai, ƙa’idodi da farillan Ubangiji shugabanmu ba.
30 “Mun yi alkawari ba za mu ba da ’ya’yanmu mata aure ga mutanen da suke kewaye da mu ba, ba kuwa za mu auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanmu maza ba.
31 “Sa’ad da maƙwabta suka kawo kayayyaki ko hatsi don su sayar a ranar Asabbaci, ba za mu saya daga gare su a ranar Asabbaci ko a rana mai tsarki ba. Kowace shekarar Asabbaci ba za mu nome ƙasa ba kuma za mu yafe kowane irin bashi.
32 “Mun ɗauka hakkin bin umarnai na ba da kashi ɗaya bisa uku na shekel kowace shekara don hidimar gidan Allahnmu. 33 Za mu tanada burodin da ake ajiye a kan tebur; za mu ba da hadayun hatsi da hadayun ƙonawa na kullum; za mu ba da hadayun Asabbatai, da na bukukkuwan Sabon Wata da na bukukkuwan da aka ƙayyade; za mu ba da hadayu masu tsarki; za mu ba da hadayun zunubi don a yi kafara domin Isra’ila; mu kuma ba da abubuwan da ake bukata dukan domin ayyukan gidan Allahnmu.
34 “Mu, firistoci, da Lawiyawa da kuma mutane, mun jefa ƙuri’a don a san lokacin da kowane iyalinmu zai kawo sadakar itace don ƙonewa a gidan Allahnmu a ƙayyadaddun lokuta a bagaden Ubangiji Allahnmu, kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka.
35 “Mun kuma ɗauka hakkin kawo nunan fari na hatsinmu da kuma na kowane itace mai ba da ’ya’ya a gidan Ubangiji kowace shekara.
36 “Kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka,*ɗan fari na ’ya’yanmu maza. Dokar Allah. Dubi Fit 13.2,12-15; 34.19,20. za mu kawo ɗan fari na ’ya’yanmu maza da na garken shanunmu, da na tumakinmu, da kuma na awakinmu a gidan Allahnmu, don firistocin da suke aikin a can.
37 “Ban da haka ma, za mu kawo wa ɗakunan ajiyar gidan Allahnmu, abincinmu na farko daga ƙasa, na hadayun hatsinmu, na ’ya’yan dukan itatuwanmu da kuma na sabon ruwan inabinmu da mai namu wa firistoci. Za mu kuma kawo zakkar hatsinmu wa Lawiyawa, gama Lawiyawa ne ke karɓan Zakka cikin dukan garuruwan da muke noma. 38 Firist wanda yake daga zuriyar Haruna zai raka Lawiyawa sa’ad da suke karɓan zakka, Lawiyawan kuma za su kawo kashi ɗaya bisa goma na zakka zuwa gidan Allahnmu, su kawo a ɗakunan ajiya na baitulmali. 39 Mutanen Isra’ila haɗe da Lawiyawa, za su kawo sadakokinsu na hatsi, sabon ruwan inabi da mai a ɗakunan ajiya inda ake ajiyar kayayyakin wuri mai tsarki da kuma inda firistoci, matsaran ƙofofi da kuma mawaƙa suke zama.
“Ba za mu ƙyale gidan Allahnmu ba.”