Zabura 16
Miktam ne*Kan magana, mai yiwuwa wata kalma ta kiɗa ce. na Dawuda.
1 Ka kiyaye ni, ya Allah,
gama a cikinka nake samun mafaka.
2 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana;
in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”
3 Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa,
su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana.
4 Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli.
Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini ba
ko in ambaci sunayensu da bakina.
5 Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na;
ka kiyaye rabona,
6 Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi;
tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa.
7 Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara;
ko da dare ma zuciyata kan koya mini.
8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.
Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.
9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;
jikina kuma zai zauna lafiya,
10 domin ba za ka yashe ni a kabari ba,
ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
11 Ka sanar da ni hanyar rai;
za ka cika ni da farin ciki a gabanka,
da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.