Zabura 17
Addu’a ce ta Dawuda.
Ka ji, ya Ubangiji, roƙona na adalci;
ka saurari kukata.
Ka kasa kunne ga addu’ata,
ba ta fitowa daga leɓuna masu ƙarya.
Bari fiffitawata tă zo daga gare ka;
bari idanunka su ga abin da yake daidai.
 
Ko ka duba zuciyata,
ka kuma bincike ni da dare,
ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba;
na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.
Game da ayyukan mutane kuwa,
ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina
daga hanyoyin tashin hankali.
Sawuna sun kama hanyoyinka
ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba.
 
Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini;
ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata.
Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki,
kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu
da hannunka na dama.
Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido;
ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka
daga mugaye waɗanda suke kai mini hari,
daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.
 
10 Sun rufe zukatansu marar tausayi,
da bakunansu suna magana da fariya.
11 Sun sa mini ido, yanzu sun kewaye ni,
a shirye suke, su jefa ni a ƙasa.
12 Suna kama da zaki mai yunwan abinci,
kamar babban zaki mai fako a maɓuya.
 
13 Ka tashi, ya Ubangiji, ka yi arangama da su, ka durƙusar da su;
ka cece ni daga mugaye ta wurin takobinka.
14 Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan,
daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne.
Kakan cika yunwan waɗanda kake so;
’ya’yansu suna da isashe
suna kuma ajiyar wadata wa ’ya’yansu.
 
15 Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka;
sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.