Zabura 28
Ta Dawuda.
1 A gare ka nake kira,
ya Ubangiji Dutsena;
kada ka yi mini kunnen ƙashi.
Gama in ka yi shiru,
zan zama kamar waɗanda suka gangara rami.
2 Ka ji kukata ta neman jinƙai
yayinda nake kira ka don neman taimako,
yayinda nake daga hannuwana
wajen Wurinka Mafi Tsarki.
3 Kada ka ja ni tare da mugaye,
tare da masu yin mugunta,
masu magana kamar ta alheri ce da maƙwabtansu
amma suna riƙe da su a zukatansu.
4 Ka sāka musu da ayyukansu
da kuma don mugun aikinsu;
ka sāka musu saboda abin da hannuwansu suka yi
ka kuma mayar musu abin da ya dace da su.
5 Da yake ba su kula da ayyukan Ubangiji
da abin da hannuwansa suka yi ba,
zai rushe su
ba kuwa zai ƙara gina su ba.
6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
gama ya ji kukata na neman jinƙai.
7 Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;
zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.
Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki
zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.
8 Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa,
kagarar ceto domin shafaffensa.
9 Ka cece mutanenka ka kuma albarkace gādonka;
ka zama mai kiwonsu ka kuma riƙe su har abada.