Zabura 29
Zabura ta Dawuda.
1 Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya,
ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.
2 Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa;
ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.
3 Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye;
Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,
Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.
4 Muryar Ubangiji mai iko ce;
muryar Ubangiji da girma take.
5 Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon.
Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.
6 Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi,
Siriyon*Wato, Dutsen Hermon kuma kamar ɗan jakin jeji.
7 Muryar Ubangiji ta buga
da walƙatar walƙiya.
8 Muryar Ubangiji ta girgiza hamada
Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.
ya kakkaɓe itatuwan kurmi.
Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”
10 Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa;
Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.
11 Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa;
Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.