Zabura 30
Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali.*Kan magana, ko kuwa faɗa Ta Dawuda.
1 Zan girmama ka Ya Ubangiji,
gama ka tsamo ni daga zurfafa
ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.
2 Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako
ka kuwa warkar da ni.
3 Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari;
ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.
4 Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa;
ku yabi sunansa mai tsarki.
5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne
amma alherinsa har matuƙa ne;
mai yiwuwa a yi kuka da dare
amma farin ciki kan zo da safe.
6 Sa’ad da nake lafiya, na ce,
“Ba zan jijjigu ba.”
7 Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri,
ka sa katangar dutsena ya tsaya daram;
amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka,
sai in cika da tsoro.
8 A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira;
a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai.
9 “Wace riba ce a hallakata,
a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami?
Ƙura za tă yabe ka ne?
Za tă iya yin shelar amincinka?
10 Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai;
Ya Ubangiji, ka zama taimakona.”
11 Ka mai da kukata ta zama rawa;
ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,
12 don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba.
Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.