Zabura 101
Ta Dawuda. Zabura ce.
1 Zan rera wa ƙauna da adalcinka;
gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo.
2 Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi,
yaushe za ka zo gare ni?
Zan bi da sha’anin gidana
da zuciya marar abin zargi
3 Ba zan kafa a gaban idanuna 1
wani abu marar kyau ba.
Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci;
ba za su manne mini ba.
4 Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni;
ba abin da zai haɗa ni da mugunta.
5 Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye
shi za a kashe;
duk mai renin wayo da mai girman kai,
ba zan jure masa ba.
6 Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar,
don su zauna tare da ni;
tafiyarsa ba ta da zargi
zai yi mini hidima.
7 Babu mai ruɗun
da zai zauna a gidana;
babu mai ƙaryan
da zai tsaya a gabana.
8 Kowace safiya zan rufe bakunan
dukan mugaye a ƙasar;
zan yanke kowane mai aikata mugunta
daga birnin Ubangiji.