Zabura 102
Addu’ar mutum mai shan wahala. Sa’ad da ya rasa ƙarfi ya kuma yi makoki a gaban Ubangiji.
1 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji;
bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka.
2 Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni
sa’ad da nake cikin damuwa.
Ka juye kunnenka gare ni;
sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri.
3 Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi;
ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta.
4 Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa;
na manta in ci abinci.
5 Saboda nishina mai ƙarfi
na rame na bar ƙasusuwa kawai.
6 Ni kamar mujiyar jeji ne,
kamar mujiya a kufai.
7 Na kwanta a faɗake; na zama
kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki.
8 Dukan yini abokan gābana suna tsokanata;
waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana.
9 Gama ina cin toka a matsayin abincina
ina kuma gauraye abin sha nawa da hawaye
10 saboda fushinka mai girma,
gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe.
11 Kwanakina suna kamar inuwar yamma;
na bushe kamar ciyawa.
12 Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada;
sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai.
13 Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona,
gama lokaci ne na nuna alheri gare ta;
ƙayyadadden lokacin ya zo.
14 Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka;
ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi.
15 Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji,
dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka.
16 Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona
ya kuma bayyana a ɗaukakarsa.
17 Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi;
ba zai ƙyale roƙonsu ba.
18 Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa,
cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji,
19 “Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa,
daga sama ya hangi duniya,
20 don yă ji nishe-nishen ’yan kurkuku
yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.”
21 Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona
yabonsa kuma a Urushalima
22 sa’ad da mutane da mulkoki
suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada.
23 Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina;
ya gajartar da kwanakina.
24 Sai na ce,
“Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah;
shekarunka suna bi cikin dukan zamanai.
25 A farkon fari ka kafa tushen duniya,
sammai kuma aikin hannuwanka ne.
26 Za su hallaka, amma za ka ci gaba;
duk za su tsufe kamar riga.
Kamar riga za ka canja su
za a kuwa zubar da su.
27 Amma kana nan yadda kake,
kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba.
28 ’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka;
zuriyarsu za su kahu a gabanka.”