Zabura 104
Yabi Ubangiji, ya raina.
 
Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai;
kana saye da daraja da ɗaukaka.
 
Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga
ya shimfiɗa sammai kamar tenti
ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye.
Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa
yana hawa a kan fikafikan iska.
Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa
harsunan wuta kuma bayinsa.
 
Ya kafa duniya a kan tussanta;
ba za a iya matsar da ita ba.
Ka rufe ta da zurfi kamar da riga
ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.
Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu
da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;
suka gudu a bisa duwatsu,
suka gangara zuwa cikin kwaruruka,
zuwa wurin da ka shirya musu.
Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa;
ba za su ƙara rufe duniya ba.
 
10 Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka;
yana gudu tsakanin duwatsu.
11 Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji;
jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu.
12 Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan;
suna rera cikin rassa.
13 Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama;
ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa.
14 Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu,
tsire-tsire domin mutum ya nome,
suna fid da abinci daga ƙasa,
15 ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna,
mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske,
abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.
16 Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai,
al’ul na Lebanon da ya shuka.
17 A can tsuntsaye suke sheƙunnansu;
shamuwa tana da gidanta a itatuwan fir.
18 Manyan duwatsu na awakin jeji ne;
tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema.
 
19 Wata ne ke ƙididdigar lokuta,
rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi.
20 Ka yi duhu, sai ya zama dare,
sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe.
21 Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta
suna kuma neman abincinsu daga Allah.
22 Rana ta fito, sai suka koma shiru;
suka koma suka kwanta a kogwanninsu.
23 Mutum yakan tafi aikinsa,
zuwa wurin aikinsa har yamma.
 
24 Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji!
Cikin hikima ka yi su duka;
duniya ta cika da halittunka.
25 Akwai teku, babba da kuma fāɗi,
cike da halittun da suka wuce ƙirga,
abubuwa masu rai babba da ƙarami.
26 A can jiragen ruwa suna kai komo,
kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.
 
27 Waɗannan duka suna dogara gare ka
don ka ba su abincinsu a daidai lokaci.
28 Sa’ad da ba su da shi,
sai su tattara shi;
sa’ad da ka buɗe hannunka,
sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau.
29 Sa’ad da ka ɓoye fuskarka,
sai su razana;
sa’ad da ka ɗauke numfashinsu,
sai su mutu su kuma koma ga ƙura.
30 Sa’ad da ka aika da Ruhunka,
sai su halittu,
su kuma sabunta fuskar duniya.
 
31 Bari ɗaukakar Ubangiji ta dawwama har abada;
bari Ubangiji yă yi farin ciki cikin aikinsa,
32 shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana,
wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi.
 
33 Zan rera ga Ubangiji dukan raina;
zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.
34 Bari tunanina yă gamshe shi,
yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.
35 Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya
mugaye kuma kada a ƙara ganinsu.
 
Yabi Ubangiji, ya raina.
 
Yabi Ubangiji.*Da Ibraniyanci Hallelu Ya; a cikin Seftuwajin wannan layi yana a farkon Zabura 105.1.

*Zabura 104:35 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; a cikin Seftuwajin wannan layi yana a farkon Zabura 105.1.