Zabura 105
Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;
ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.
Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki;
bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
 
Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi,
mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar,
Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa,
Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa.
Shi ne Ubangiji Allahnmu;
kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya.
 
Yana tuna da alkawarinsa har abada,
maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,
alkawarin da ya yi da Ibrahim,
rantsuwar da ya yi wa Ishaku.
10 Ya tabbatar da shi ga Yaƙub a matsayin ƙa’ida,
Isra’ila a matsayin madawwamin alkawari,
11 “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana
a matsayin rabo za ka yi gādo.”
 
12 Sa’ad da suke kima kawai,
kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,
13 suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma,
daga masarauta zuwa wata.
14 Bai bar kowa yă danne su ba;
saboda su, ya tsawata wa sarakuna,
15 “Kada ku taɓa shafaffena;
kada ku yi wa annabawa lahani.”
 
16 Ya sauko da yunwa a kan ƙasa
ya kuma lalace dukan tanadinsu na abinci;
17 ya kuma aiki mutum a gabansu,
Yusuf, da aka sayar a matsayin bawa.
18 Suka raunana ƙafafunsa da sarƙa
aka sa wuyansa cikin ƙarafa,
19 sai abin da ya rigafaɗi ya cika
sai da maganar Ubangiji ta tabbatar da shi mai gaskiya.
20 Sarki ya aika aka kuma sake shi,
mai mulkin mutane ya ’yantar da shi.
21 Ya mai da shi shugaban gidansa,
mai mulki a bisa dukan abin da ya mallaka,
22 don yă umarci sarakunansa yadda ya ga dama
yă kuma koya wa dattawa hikima.
 
23 Sa’an nan Isra’ila ya shiga Masar;
Yaƙub ya yi zama kamar baƙo a ƙasar Ham.
24 Ubangiji ya mai da mutanensa suka yi ta haihuwa;
ya sa suka yi yawa suka fi ƙarfin maƙiyansu,
25 waɗanda ya juya zukatansu su ƙi mutanensa
don su haɗa baki a kan bayinsa.
26 Ya aiki Musa bawansa,
da Haruna, wanda ya zaɓa.
27 Suka yi mu’ujizansa a cikinsu,
abubuwan mamakinsa a cikin ƙasar Ham.
28 Ya aiko da duhu ya kuma sa ƙasar tă yi duhu,
ba domin sun yi tawaye a kan maganarsa ba?
29 Ya mai da ruwaye suka zama jini,
ya sa kifayensu suka mutu.
30 Ƙasarsu ta yi ta fid da kwaɗi,
waɗanda suka haura cikin ɗakunan kwana na masu mulkinsu.
31 Ya yi magana, sai tarin ƙudaje suka fito,
cinnaku kuma ko’ina a ƙasar.
32 Ya mai da ruwan samansu ya zama ƙanƙara,
da walƙiya ko’ina a ƙasarsu;
33 ya lalace inabinsu da itatuwan ɓaurensu
ya ragargaza itatuwan ƙasarsu.
34 Ya yi magana, sai fāri ɗango suka fito,
fāran da ba su ƙidayuwa;
35 suka cinye kowane abu mai ruwan kore a cikin ƙasarsu,
suka cinye amfanin gonarsu
36 Sa’an nan ya karkashe dukan ’yan fari a cikin ƙasarsu,
nunan fari na dukan mazantakarsu.
37 Ya fitar da Isra’ila, ɗauke da azurfa da zinariya,
kuma daga cikin kabilansu babu wani da ya kāsa.
38 Masar ta yi murna sa’ad da suka tafi,
saboda tsoron Isra’ila ya fāɗo musu.
 
39 Ya shimfiɗa girgije kamar mayafi,
da kuma wuta don ta ba su haske da dare.
40 Suka roƙa, ya kuwa ba su makware
ya kuma ƙosar da su da abinci daga sama.
41 Ya buɗe dutse, sai ruwa ya ɓulɓulo,
kamar kogi ya gudu zuwa cikin hamada.
 
42 Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki
da ya ba wa bawansa Ibrahim.
43 Ya fitar da mutanensa da farin ciki,
zaɓaɓɓunsa da sowa ta farin ciki;
44 ya ba su ƙasashen al’ummai,
suka kuma sami gādon abin da waɗansu sun sha wahala a kai,
45 don su kiyaye farillansa
su kuma kiyaye dokokinsa.
 
Yabo ga Ubangiji.*Da Ibraniyanci Hallelu Ya

*Zabura 105:45 Da Ibraniyanci Hallelu Ya