Zabura 106
Yabi Ubangiji.*Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka kuma a aya 48.
 
Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
 
Wane ne zai furta manyan ayyukan Ubangiji
ko yă furta cikakken yabonsa?
Masu albarka ne waɗanda suke yin adalci,
waɗanda kullum suke yin abin da yake daidai.
 
Ka tuna da ni, ya Ubangiji, sa’ad da ka nuna alheri ga mutanenka,
ka zo ka taimake ni sa’ad da ka cece su,
don in ji daɗin nasarar zaɓaɓɓunka,
don in sami rabo cikin farin cikin al’ummarka
in kuma shiga gādonka cikin yin yabo.
 
Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi;
mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta.
Sa’ad da kakanninmu suke a Masar,
ba su damu da mu’ujizanka ba;
ba su tuna yawan alheranka ba,
suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku.
Duk da haka ya cece su saboda sunansa,
don yă sanar da ikonsa mai girma.
Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe;
ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada.
10 Ya cece su daga hannun maƙiyi;
daga hannun abokin gāba ya fanshe su.
11 Ruwaye suka rufe abokan gābansu;
babu ko ɗaya da ya tsira.
12 Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa
suka kuma rera yabonsa.
 
13 Amma nan da nan suka manta abin da ya yi
ba su kuwa jira shawararsa ba.
14 A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su
a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.
15 Sai ya ba su abin da suka roƙa,
amma ya aika musu da muguwar cuta.
 
16 A sansani suka ji kishin Musa
da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe.
17 Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan
ta binne iyalin Abiram.
18 Wuta ta ƙuno a cikin mabiyansu;
harshen wuta ya cinye mugaye.
19 A Horeb suka yi ɗan maraƙi
suka yi wa gunkin zubi daga ƙarfe sujada.
20 Suka sauke Ɗaukakarsu
saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa.
21 Suka manta da Allahn da ya cece su,
wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar,
22 mu’ujizai a ƙasar Ham
ayyukan banrazana a Jan Teku.
23 Don haka ya ce zai hallaka su,
amma Musa, zaɓaɓɓensa,
ya yi godo a gabansa
don yă kau da hasalarsa daga hallaka su.
 
24 Sai suka rena ƙasa mai ni’ima;
ba su gaskata alkawarinsa ba.
25 Suka yi gunaguni a tentunansu
ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba.
26 Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu
cewa zai sa su mutu a cikin hamada,
27 ya sa zuriyarsu su mutu a cikin al’ummai
ya kuma watsar da su cikin dukan ƙasashe.
 
28 Suka haɗa kai da Ba’al-Feyor
suka kuma ci hadayun da aka miƙa wa allolin da ba su da rai;
29 suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu,
sai annoba ta ɓarke a cikinsu.
30 Amma Finehas ya miƙe tsaye ya ɗauki mataki,
sai annobar ta daina.
31 An ayana masa wannan a matsayin adalci
har zamanai marar matuƙa masu zuwa.
32 A ruwan Meriba suka ba Ubangiji fushi,
sai wahala ta zo wa Musa saboda su;
33 saboda sun yi tayarwa a kan Ruhun Allah,
har mugayen kalmomi suka fito daga leɓunan Musa.
 
34 Ba su hallakar da mutanen
yadda Ubangiji ya umarce su ba,
35 amma suka yi cuɗanya da al’ummai
suka ɗauki al’adunsu.
36 Suka yi wa gumakansu sujada,
waɗanda suka zama tarko gare su.
37 Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya
’yan matansu kuma ga aljanu.
38 Suka zub da jini marar laifi,
jinin ’ya’yansu maza da mata,
waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana,
ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.
39 Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi;
ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci.
 
40 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa
ya ji ƙyamar gādonsa.
41 Ya miƙa su ga al’ummai,
maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu.
42 Abokan gābansu suka danne su
suka sa su a ƙarƙashin ikonsu.
43 Sau da yawa ya cece su,
amma sun nace su yi tawaye
suka kuma lalace cikin zunubinsu.
44 Amma ya lura da wahalarsu
sa’ad da ya ji kukansu;
45 saboda su ya tuna da alkawarinsa
kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.
46 Ya sa aka ji tausayinsu
a wurin dukan waɗanda suka kame su.
 
47 Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu,
ka kuma tattara mu daga al’ummai,
don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya
mu kuma ɗaukaka cikin yabonka.
 
 
48 Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,
daga madawwami zuwa madawwami.
 
Bari dukan mutane su ce, “Amin!”
 
Yabo ga Ubangiji.

*Zabura 106:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka kuma a aya 48.