Zabura 142
Maskil ne*Kan maganar, mai yiwuwa kalmar waƙa ce. ta Dawuda. Sa’ad da yake cikin kogo. Addu’a ce.
1 Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji;
na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai.
2 Na kawo gunagunina a gabansa;
a gabansa na faɗa wahalata.
3 Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina,
kai ne wanda ya san hanyata.
A hanyar da nake tafiya
mutane sun kafa mini tarko.
4 Duba ta damata ka gani;
babu wanda ya kula da ni.
Ba ni da mafaka;
babu wanda ya kula da raina.
5 Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;
Na ce, “Kai ne mafakata,
rabona a ƙasar masu rai.”
6 Ka saurari kukata,
gama ina cikin matsananciyar bukata;
ka cece ni daga waɗanda suke fafarata,
gama sun fi ni ƙarfi sosai.
7 Ka ’yantar da ni daga kurkuku,
don in yabi sunanka.
Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni
saboda alherinka gare ni.