Zabura 143
Zabura ta Dawuda.
1 Ya Ubangiji, ka ji addu’ata,
ka saurari kukata don neman jinƙai;
cikin amincinka da adalcinka
ka amsa mini.
2 Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a,
gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka.
3 Abokin gāba yana fafarata,
ya murƙushe ni har ƙasa;
ya sa ina zama a cikin duhu
kamar waɗanda suka mutu tun tuni.
4 Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina
zuciyata ta damu ƙwarai.
5 Na tuna da kwanakin baya
na yi tunani a kan dukan ayyukanka
na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi.
6 Na buɗe hannuwana gare ka;
raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa.
Sela
7 Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji;
ƙarfina ya ƙare.
Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni
in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami.
8 Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,
gama na sa zuciyata a gare ka.
Ka nuna mini hanyar da zan bi,
gama a gare ka na miƙa raina.
9 Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji,
gama na ɓoye kaina a gare ka.
10 Ka koya mini in yi nufinka,
gama kai ne Allahna;
bari nagarin Ruhunka
yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.
11 Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina;
a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala.
12 A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana;
ka hallaka dukan maƙiyana,
gama ni bawanka ne.