14
Ɗan Ragon da 144,000
Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu. Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu. Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya. Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon. Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne.
Mala’iku uku
Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”
Mala’ika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan al’ummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.”
Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu, 10 shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon. 11 Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.” 12 Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu.
13 Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.”
“I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.
Girbin duniya
14 Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum”*Dubi Dan 7.13. tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa. 15 Sai wani mala’ika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.” 16 Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya.
17 Wani mala’ika kuma ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da lauje mai kaifi. 18 Har yanzu, wani mala’ika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan ’ya’yan inabi daga kuringar inabin duniya, domin ’ya’yan inabin sun nuna.” 19 Mala’ikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara ’ya’yan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah. 20 Aka tattake su a wurin matsin inabi a bayan gari, jini kuwa ya yi ta gudana daga wurin matsin inabi tsayinsa ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, nisansa kuma ya kai wajen kilomita 300.

*14:14 Dubi Dan 7.13.