Rut
1
Na’omi ta rasa mijinta da ’ya’yanta maza
1 A kwanakin da mahukunta suke mulki*A gargajiyance alƙalai an yi yunwa a ƙasar, sai wani mutum daga Betlehem a Yahuda tare da matarsa da ’ya’yansu maza biyu, suka tafi su yi zama na ɗan lokaci a ƙasar Mowab. 2 Sunan mutumin, Elimelek ne, sunan matarsa Na’omi; sunayen ’ya’yan nan nasu biyu, su ne Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Betlehem ta Yahuda. Suka kuwa tafi Mowab suka zauna a can.
3 To, Elimelek mijin Na’omi ya rasu, aka bar ta da ’ya’yanta maza biyu. 4 Suka auri mata Mowabawa, sunan ɗaya Orfa ɗayan kuma Rut. Bayan sun zauna a can kamar shekara goma, 5 sai Malon da Kiliyon suka mutu su ma, aka kuma bar Na’omi babu ’ya’yanta maza biyu da kuma mijinta.
Na’omi da Rut sun dawo Betlehem
6 Sa’ad da ta ji a Mowab cewa Ubangiji ya zo don yă taimaki mutanensa ta wurin tanada musu da abinci, sai Na’omi tare da surukanta suka shirya su koma gida daga can. 7 Tare da surukanta biyu suka bar inda suka zauna suka kuma kama hanya da za tă komar da su zuwa ƙasar Yahuda.
8 Sai Na’omi ta ce wa surukanta biyu, “Ku koma, kowannenku, zuwa gidan mahaifiyarta. Bari Ubangiji yă nuna muku alheri yadda kuka nuna wa matattun nan da kuma gare ni. 9 Bari Ubangiji yă sa kowannenku ta sami hutu a gidan wani miji.”
Sa’an nan ta sumbace su suka kuma yi kuka da ƙarfi 10 suka ce mata, “Za mu tafi tare da ke zuwa ga mutanenki.”
11 Amma Na’omi ta ce, “Ku koma gida, ’ya’yana mata. Don me za ku tafi tare da ni? Zan ƙara samun waɗansu ’ya’ya maza da za su zama mazanku ne? 12 Ku koma gida ’ya’yana mata; na tsufa ainun da zan sāke samun wani miji. Ko ma na yi tsammani har yanzu ina da bege, ko ma na sami miji a wannan dare na kuma haifi ’ya’ya maza, 13 za ku jira sai sun yi girma? Za ku ci gaba da kasance babu aure saboda su? A’a, ’ya’yana mata. Ina da baƙin ciki ƙwarai fiye da ku, domin hannun Ubangiji ya yi gāba da ni!”
14 A kan wannan suka sāke ɓarke da kuka. Sa’an nan Orfa ta sumbaci surukarta ta yi bankwana, amma Rut ta manne mata.
15 Sai Na’omi ta ce, “Duba, ’yar’uwanki ta koma zuwa ga mutanenta da kuma allolinta. Ki koma tare da ita.”
16 Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna. 17 Inda za ki mutu zan mutu, zan mutu a can kuma za a binne ni. Bari Ubangiji ya hukunta ni da tsanani sosai, in wani abu in ba mutuwa ce ta raba ke da ni ba.” 18 Sa’ad da Na’omi ta gane cewa Rut ta ƙudura tă tafi tare da ita, sai ta daina nema tă koma.
19 Saboda haka matan biyu suka ci gaba da tafiya sai da suka isa Betlehem. Da suka isa Betlehem, sai dukan garin ya ruɗe saboda su, matan kuwa suka ce, “Na’omi ce wannan kuwa?”
20 Ta ce musu, “Kada ku kira ni Na’omi.†Na’omi yana nufin mai daɗi; haka ma a aya 21. Ku kira ni Mara‡Mara yana nufin ɗaci. gama Maɗaukaki§Da Ibraniyanci an rubuta Shaddai ne a nan. ya sa raina ya yi ɗaci sosai. 21 In tafi cikakke, amma Ubangiji ya dawo da ni ba kome. Don me kuke kirana Na’omi? Ubangiji ya wahalshe*Ko kuwa ba da shaida gāba da ni. ni, Maɗaukaki ya kawo mini masifa.”
22 Na’omi fa ta koma daga Mowab tare da Rut mutuniyar Mowab, surukarta, suka kai Betlehem a lokacin da ake fara girbin sha’ir.