2
Rut ta sadu da Bowaz
To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz.
Sai Rut mutuniyar Mowab ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi gonaki in yi kala raguwar hatsi a bayan duk wanda na sami tagomashi daga gare shi.”
Na’omi ta ce mata, “Ki je, ’yata.” Saboda haka ta tafi ta fara kala a gonaki a bayan masu girbi. Sai ya zamana, ta sami kanta tana aiki a gonar da take ta Bowaz, wanda yake daga dangin Elimelek.
Sai ga Bowaz ya iso daga Betlehem ya gai da masu girbi, “Ubangiji yă kasance tare da ku!”
Sai suka amsa, “Ubangiji yă albarkace ka!”
Sai Bowaz ya tambayi shugaban masu girbinsa, “Wace yarinya ce wannan?”
Shugaban ya amsa, “Ita ce mutuniyar Mowab da ta zo daga Mowab tare da Na’omi. Ta ce, ‘Ina roƙo a bar ni in bi bayan masu girbin in yi kala.’ Haka ta shiga cikin gonar ta kuwa yi aiki tun da safe har zuwa yanzu, sai ɗan hutun da ta yi kaɗan.”
Saboda haka Bowaz ya ce wa Rut, “’Yata, ki saurare ni. Kada ki tafi ki yi kala a wani gona, kada kuma ki tafi daga nan. Ki tsaya nan tare da ’yan matana bayi. Ki lura da gonar da mutanena suke girbi, ki bi su tare da ’yan matana. Na riga na faɗa wa mazan kada su taɓa ke. Kuma duk sa’ad da kika ji ƙishirwa, ki tafi ki ɗebo ruwa daga tulunan da mazan suka cika.”
10 Jin haka, sai ta rusuna da fuskata har ƙasa ta ce, “Me ya sa na sami irin wannan tagomashi a idanunka da har ka lura da ni, ni da nake baƙuwa?”
11 Bowaz ya amsa, “An faɗa mini duka game da abin kika yi domin surukarki tun mutuwar mijinki, yadda kika bar mahaifinki da mahaifiyarki da kuma ƙasarki kika zo ki yi zama da mutanen da ba ki taɓa sani ba. 12 Bari Ubangiji yă sāka maka saboda abin da ka yi. Bari Ubangiji, Allah na Isra’ila yă sāka maka a yalwace, a ƙarƙashin fikafikan da ka sami mafaka.”
13 Ta ce, “Bari in ci gaba da samun tagomashi a idanunka ranka yă daɗe. Ka ta’azantar da ni ka kuma yi wa baranyarka magana mai alheri ko da yake ban kai matsayi ɗaya daga cikin bayinka ’yan mata ba.”
14 A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.”
Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa. 15 Da ta tashi don tă yi kala, sai Bowaz ya yi umarni wa samarinsa cewa, “Ko ta tara daga cikin dammuna, kada ku wulaƙanta ta. 16 Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.”
17 Saboda haka Rut ta yi kala a gonar har yamma. Sa’an nan ta sussuka hatsin sha’ir da ta kalata ta sami kamar efa.* Wato, kusan bushel uku bisa biyar (Kamar lita 22) 18 Ta ɗauka ta koma gari sai surukarta ta ga yawan abin da ta kalato. Rut kuma ta fitar da ragowar abin da ta ci bayan ta ƙoshi ta ba ta.
19 Surukarta ta tambaye ta, “Ina kika yi kala a yau? Ina kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga mutumin nan ta ya lura da ke!”
Sai Rut ta faɗa wa surukarta game da wurin wanda ta yi ta aiki. Ta ce, “Sunan mutumin da na yi aiki da shi a yau Bowaz ne.”
20 Sai Na’omi ta ce wa surukarta, “Ubangiji yă yi masa albarka! Bai daina nuna alheri ga masu rai da matattu ba.” Ta ƙara da cewa, “Wannan mutum danginmu ne na kusa; shi ɗaya daga cikin danginmu mai fansa.”
21 Sa’an nan Rut mutuniyar Mowab ta ce, “Ya ma ce mini, ‘Ki riƙa bin ma’aikatana sai sun ƙare yin girbin dukan hatsina.’ ”
22 Na’omi ta ce wa Rut surukarta, “Zai fi miki kyau, ’yata ki riƙa tafiya da ’yan matansa, domin a gonar wani dabam mai yiwuwa a yi miki lahani.”
23 Saboda haka Rut ta tsaya kusa da bayi mata na Bowaz don tă yi kala sai da girbin sha’ir da na alkama suka ƙare. Ta kuwa zauna tare da surukarta.

*2:17 Wato, kusan bushel uku bisa biyar (Kamar lita 22)