2
Yawo a cikin hamada
Sai muka juya muka kama hanya, muka nufi hamada, ta hanyar Jan Teku* yadda Ubangiji ya umarce ni. Da daɗewa muka yi ta yawo kewaye da ƙasar tudun Seyir.
Sai Ubangiji ya ce mini, “Kun yi ta yawo kewaye da ƙasar tudun nan da daɗewa; yanzu ku juya, ku nufi arewa. Ka ba wa mutane waɗannan umarnai, ka ce, ‘Kuna gab da wucewa cikin yankin ’yan’uwanku, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Za su ji tsoronku, amma ku yi hankali kada ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku wata ƙasa daga cikinsu ba, ba ma wadda za tă iya isa ku sa ƙafarku a kai. Na ba wa Isuwa ƙasar tudu ta Seyir, ta zama tasa. Duk abincin za ku ci, da ruwan da za ku sha, za ku biya su.’ ”
Ubangiji Allahnku ya albarkace ku cikin dukan aikin hannuwanku. Ya kiyaye ku cikin tafiyarku a duk fāɗin hamada. Waɗannan shekaru arba’in Ubangiji Allahnku ya kasance tare da ku, ba kuwa kun rasa wani abu ba.
Saboda haka muka ci gaba, muka wuce ’yan’uwanmu, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Muka bar hanyar Araba, wadda ta haura daga Elat da Eziyon Geber, muka nufi wajen hamadar Mowab.
Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ku dami Mowabawa, ko ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku wani sashe na ƙasarsu ba. Na ba da Ar ga zuriyar Lot, ta zama mallakarsu.”
10 (Emawa, mutane ne masu ƙarfi da kuma yawa, suna kuma da tsayi kamar Anakawa, dā sun zauna a can. 11 Kamar Anakawa, su ma an ɗauka su Refahiyawa ne, amma Mowab suna kiransu Emawa. 12 Haka ma Horiyawa, a dā sun zauna a Seyir, amma zuriya Isuwa suka kore su. Suka hallaka Horiyawa da suke kafinsu, suka kuma zauna a wurinsu, kamar dai yadda Isra’ila ta yi a ƙasar da Ubangiji ya ba su a matsayin mallaka.)
13  Ubangiji kuwa ya ce, “Yanzu ku tashi ku ƙetare Kwarin Zered.” Sai muka ƙetare kwarin.
14 Dukan shekarun da muka yi a tafiyarmu daga Kadesh Barneya zuwa lokacin da muka ƙetare Kwarin Zered, sun kai shekaru talatin da takwas. A lokacin, wannan tsara gaba ɗaya ta mutanen da suka isa yaƙi sun mutu daga sansani, yadda Ubangiji ya rantse musu. 15 Hannun Ubangiji ya yi gāba da su sai da ya hallaka su ƙaƙaf daga sansani.
16 To, sa’ad da na ƙarshe cikin waɗannan mayaƙa a cikin mutanen ya rasu, 17 sai Ubangiji ya ce mini, 18 “Yau za ku wuce ta yankin Mowab a Ar. 19 Sa’ad da kuka iso kusa da Ammonawa, kada ku dame su, ko ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku mallakar wata ƙasar da take ta Ammonawa ba. Na riga na ba da ita mallaka ga zuriyar Lot.”
20 (Wannan ita ma a ɗauka ta a matsayin ƙasar Refahiyawa waɗanda dā sun zauna a can ne; amma Ammonawa suna ce da su Zamzummawa. 21 Mutane ne masu ƙarfi da kuma yawa, suna kuma da tsayi kamar Anakawa. Ubangiji ya hallaka su daga gaban Ammonawa, waɗanda suka kore su, suka kuma zauna a wurinsu. 22  Ubangiji ya yi daidai yadda ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a ƙasar Seyir, sa’ad da ya hallaka Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su, suka zauna a wurinsu. Har wa yau, zuriyar Isuwa ne suke zama a can. 23 Kusan abu ɗaya ya faru, sa’ad da Kaftorawa daga ƙasar Kaftor suka hallaka Awwiyawa, waɗanda dā suke zaune a yankin ƙauyukan da suke kewaye da Gaza. Suka zauna a wurinsu.)
Cin Sihon sarkin Heshbon da yaƙi
24 “Ku fito yanzu ku ƙetare Kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon mutumin Amoriyawa a hannunku, na kuma ba da sarkin Heshbon da ƙasarsa. Ku fara mallake ta, ku kuma yi yaƙi da shi. 25 A wannan rana zan fara sa tsoro da fargabanku a kan dukan al’ummai, a ƙarƙashin sama. Za su ji labarinku, za su yi rawan jiki, su kuma damu saboda ku.”
(Ƙidaya 21.21-30)
26 Daga hamadar Kedemot, na aiki ’yan saƙo zuwa wurin Sihon sarkin Heshbon, a kan ina neman zaman lafiya, ina cewa, 27 “Bari mu wuce cikin ƙasarka. Za mu bi ta kan hanya ne kaɗai; ba za mu ratse dama ko hagu ba. 28 Ka sayar mana da abincin da za mu ci, da kuma ruwan da za mu sha a farashinsu na azurfa. Ka dai bar mu mu wuce ta ƙasarka kawai, 29 kamar yadda zuriyar Isuwa, waɗanda suke zaune a Seyir, da Mowabawa, waɗanda suke zaune a Ar, suka yardar mana, gama muna so mu ƙetare Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu.” 30 Amma Sihon sarkin Heshbon ya ƙi yă bar mu mu wuce a ciki. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruhunsa ya taurare don yă ba da shi a hannuwanku kamar yadda ya yi yanzu.
31  Ubangiji ya ce mini, “Duba, na fara ba da Sihon da ƙasarsa gare ku. Yanzu ku fara cinta, ku kuma mallake ƙasarsa.”
32 Sa’ad da Sihon da dukan sojojinsa suka fito don su sadu da mu, a yaƙi, a Yahaz, 33 sai Ubangiji Allahnmu ya ba da shi gare mu, muka kuwa buga shi tare da ’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa. 34 A wannan lokaci mun ci dukan biranensa, muka kuma hallaka su, maza, mata da kuma yara. Ba mu bar wani da rai ba. 35 Amma muka washe, muka kuma kwasa shanu da kuma ganima daga biranen wa kanmu. 36  Ubangiji Allahnmu ya taimake mu muka ci Arower wadda take a gefen Kwarin Arnon, da garin da yake a cikin kwarin, har zuwa Gileyad. Babu garin da ya gaggare mu. 37 Amma bisa ga umarnin Ubangiji Allahnmu, ba ku yi kusa da wata ƙasar Ammonawa, ko ƙasar da take gefen kwarin kogin Yabbok, ko kuwa wadda take kewaye da birane cikin tuddai ba.
* 2:1 Da Ibraniyanci Yam Suf; wato, Tekun Iwa.