3
Cin Og sarkin Bashan da yaƙi
(Ƙidaya 21.31-35)
Biye da wannan muka juya muka haura ta hanyar wajen Bashan, inda Og, sarkin Bashan tare da dukan mayaƙansa suka fito don su sadu da mu a yaƙi, a Edireyi. Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ji tsoronsa, gama na riga na miƙa shi da dukan mayaƙansa da kuma ƙasarsa gare ka. Yi masa abin da ka yi wa Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon.”
Saboda haka Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, sarkin Bashan da dukan mayaƙansa a hannuwanmu. Muka karkashe su, ba mu bar wani da rai ba. A wannan lokaci muka kwashe dukan biranensa. Babu ɗaya daga birane sittin da ba mu ɗauke daga gare su ba, dukan yankin Argob, masarautar Og a Bashan. Dukan biranen nan masu katanga da suke da tsayi masu ƙofofi da ƙyamare, akwai kuma manya ƙauyukan da ba su da katanga. Muka hallaka su ƙaƙaf, kamar yadda muka yi wa Sihon sarkin Heshbon, muka hallaka kowace birni, maza, mata da yara. Amma dukan dabbobin da kuma ganimar daga biranensu muka kwaso wa kanmu.
A lokacin ne muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato, ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga Kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon. (Hermon ne Sidoniyawa suke kira Siriyon, Amoriyawa kuwa suna kira shi Senir.) 10 Muka kama dukan biranen da suke kan tudu, da dukan Gileyad, da dukan Bashan, har zuwa Saleka da Edireyi, biranen masarautar Og a Bashan. 11 (Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.)
Rabawa ƙasar
(Ƙidaya 32.1-42)
12 Cikin ƙasar da muka kwasa a lokacin, na ba wa mutanen Ruben da mutanen Gad yankin arewa na Arower ta Kwarin Arnon, haɗe da rabin ƙasar tudu ta Gileyad, tare da biranenta. 13 Sai kuma na ba wa rabin kabilar Manasse sauran rabin ƙasar tudu ta Gileyad da kuma dukan Bashan, masarautar Og (Wato, dukan yankin ƙasan nan na Argob a Bashan da dā ake kira ƙasar Refahiyawa. 14 Yayir na zuriyar Manasse ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawwot Yayir.)* 15 Na kuma ba da Gileyad ga Makir. 16 Amma ga mutanen Ruben da mutanen Gad, na ba da yankin da ya tashi daga Gileyad, ya gangara zuwa Kwarin Arnon (tsakiyar kwarin kuwa shi ne iyaka) ya fita zuwa Kogin Yabbok, wanda yake shi ne iyakar Ammonawa. 17 Iyakarsa daga yamma kuwa shi ne Urdun a Araba, daga Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri) a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas.
18 Na umarce ku a lokacin na ce, “Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban ’yan’uwanku, Isra’ilawa. 19 Amma matanku, yaranku da dabbobinku (na sani kuna da dabbobi masu yawa), su ne za ku bari a garuruwan da na ba ku, 20 sai Ubangiji ya ba da hutu ga sauran ’yan’uwanku, yadda ya yi da ku, su ma suka sami ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su, a ƙetaren Urdun, sa’an nan kowannenku zai komo ga mallakar da na ba ku.”
An hana Musa ƙetare Urdun
21 A lokacin nan na umarci Yoshuwa na ce, “Da idanunka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan sarakuna biyu. Haka Ubangiji zai yi da dukan masarautai a can, inda za ku. 22 Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku zai yi yaƙi dominku.”
23 A lokacin, na roƙi Ubangiji na ce, 24 “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka fara nuna wa bawanka ɗaukakarka da ikonka. Akwai wani allah a sama ko a duniya, wanda zai aikata waɗannan manyan ayyukan kamar ka? 25 Ina roƙonka, bari in ƙetare in ga ƙasa mai kyau ɗin nan a ƙetaren Urdun, wannan ƙasar mai kyau ta tuddai, da kuma Lebanon.”
26 Amma saboda ku, Ubangiji ya yi fushi da ni, bai kuwa saurare ni ba. Sai Ubangiji ya ce, “Ya isa haka, kada ka ƙara yin magana da ni game da wannan batu. 27 Haura zuwa ƙwanƙolin Fisga, ka dubi ƙasar da idanunka daga kowane gefe, yamma, da arewa, da kudu, da kuma gabas, gama ba za ka ƙetare wannan Urdun ba. 28 Amma ka umarci Yoshuwa, ka ƙarfafa shi, ka kuma ba shi ƙarfin gwiwa, gama shi ne zai jagoranci wannan mutane su haye, yă kuma ba su gādon ƙasar da za ka gani.” 29 Sai muka zauna a kwari kusa da Bet-Feyor.
* 3:14 Ko kuwa kira mazaunin Yayir