4
An umarta a yi biyayya
To, ku ji, ya Isra’ila, ku kasa kunne ga ƙa’idodi da dokokin da nake shirin koya muku. Ku bi su domin ku yi tsawon rai, ku kuma shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku yake ba ku. Kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin abin da nake umarce ku. Amma ku kiyaye umarnan nan na Ubangiji Allahnku, da na ba ku.
Da idanunku, kun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba’al-Feyor. Yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka waɗansu daga cikinku waɗanda suka yi wa Ba’al-Feyor sujada, Amma ku da kuka manne ga Ubangiji Allahnku, kuna da rai har wa yau.
Ga shi, na koya muku ƙa’idodi da dokoki, yadda Ubangiji Allahna ya umarce ni, don ku bi su a ƙasar da za ku shiga ku mallaki. Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al’ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa’ad da al’ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, “Ba shakka, wannan babbar al’umma tana da hikima da ganewa.” Wace al’umma ce mai girma haka wadda allolinta take kusa da su yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu a duk sa’ad da muka yi addu’a gare shi? Wace al’umma ce mai girma haka wadda take da ƙa’idodi da dokoki masu adalci kamar waɗannan ƙunshin dokokin da nake sa a gabanku a yau?
Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku. 10 Ku tuna da ranar da kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da ya ce mini, “Ka tara mutane a gabana, don su ji maganata, su koya yin mini bangirma muddin ransu a ƙasar, su kuma iya koyar da su ga ’ya’yansu.” 11 Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutse yayinda yana cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma baƙin gizagizai da kuma baƙin duhu. 12 Sai Ubangiji ya yi magana daga wutar. Kuka ji furcin kalmomin, amma ba ku ga siffar kome ba, sai dai murya kaɗai kuka ji. 13 Ya furta alkawarinsa gare ku, Dokoki Goma, waɗanda ya umarce ku ku bi, ya kuma rubuta su a alluna biyu. 14 Sa’an nan Ubangiji ya umarce ni a wannan lokaci, in koya muku ƙa’idodi da dokokin da za ku bi a ƙasar da kuke hayewa Urdun don mallake.
An hana bautar gumaka
15 Ba ku ga wata siffa a ranar da Ubangiji ya yi magana da ku a Horeb daga wuta ba. Saboda haka ku lura da kanku sosai, 16 don kada ku lalace, ku kuma yi wa kanku gunki, siffa ta wani kama, ko a kamannin namiji, ko kuwa ta mace, 17 ko a kamannin wata dabba a duniya, ko na wani tsuntsun da yake tashi a sama, 18 ko kuwa a kamannin wata halittar da take rarrafe a ƙasa, ko na wani kifi a cikin ruwaye a ƙarƙashi. 19 Sa’ad da kuka ɗaga ido kuka kali sama, kuka ga rana da wata, da taurari, da dukan halittun sama, sai ku kula fa, kada ku jarrabtu, ku ce za ku yi musu sujada, ko ku bauta musu; abubuwan nan Ubangiji Allahnku ne ya rarraba wa dukan al’umman da suke ko’ina a ƙarƙashin sararin sama. 20 Amma ku, Ubangiji ya ɗauke ku, ya fid da ku daga matuya mai narken ƙarfe, wato, daga Masar, domin ku zama jama’arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau.
21  Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, ya kuma yi rantsuwa cewa ba zan haye Urdun, in shiga ƙasan nan mai kyau da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo ba. 22 Zan mutu a wannan ƙasa; ba zan haye Urdun ba; amma kuna gab da ƙetarewa, ku mallaki wannan ƙasa mai kyau. 23 Ku yi hankali kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku; kada fa ku yi wa kanku gunki a kamannin wani abin da Ubangiji Allahnku ya hana. 24 Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai ƙuna, Allah ne mai kishi.
25 Bayan kun haifi ’ya’ya da jikoki, kuka kuma zauna na dogon lokaci a ƙasar, in har kuka lalace, kuka kuma yi wani irin gunki, kuna aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku, kuna kuma sa shi fushi. 26 Yau, na kira sama da duniya, su zama shaidata a kanku. Idan kuka yi rashin biyayya, lalle za ku hallaka nan da nan daga ƙasar da kuke ƙetare Urdun ku gāda. Ba za ku daɗe a cikinta ba, amma za a kawar da ku ƙaƙaf. 27  Ubangiji zai watsar da ku a cikin mutane, ɗan kaɗan ne kaɗai za su ragu a cikin al’umman da Ubangiji zai kai ku. 28 A can za ku bauta wa allolin da mutum ya yi, na itace da dutse da ba sa gani, ba sa ji, ba sa ci, ba kuma iya sansanawa. 29 Amma daga can in kuka nemi Ubangiji Allahnku, da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, za ku same shi. 30 Sa’ad da kuke cikin wahala saboda waɗannan abubuwan da suka same ku nan gaba, to, sai ku juyo ga Ubangiji Allahnku, ku kuma yi masa biyayya. 31 Gama Ubangiji Allahnku, Allah ne mai jinƙai; ba zai yashe ku ko yă hallaka, ko kuma yă manta da alkawarin da ya yi da kakanninku, wanda ya tabbatar da su da rantsuwa ba.
Ubangiji Allah ne
32 Ku bincika dukan tarihi mana, tun daga lokacin da Allah ya halicci mutane a cikin duniya har yă zuwa yanzu; ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa? 33 Akwai waɗansu mutanen da suka taɓa jin muryar Allah yana magana daga wuta, kamar yadda kuka ji har suka rayu? 34 Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?
35 An nuna muku dukan waɗannan abubuwa saboda ku san cewa Ubangiji, shi ne Allah; ban da shi, babu wani. 36 Daga sama ya sa kuka ji muryarsa, don yă hore ku. A duniya ya nuna muku wutarsa mai girma, kuka kuma ji kalmominsa daga wuta. 37 Domin ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓi zuriyarsu a bayansu, ya fitar da ku daga Masar ta wurin kasancewarsa da kuma ƙarfinsa mai girma, 38 don yă fitar da ku a gaban al’ummai da suka fi ku girma da kuma ƙarfi, ya kawo ku cikin ƙasarsu, don yă ba ku ita ta zama gādonku, kamar yadda yake a yau.
39 Ku sani, ku kuma riƙe a zuciya a wannan rana, cewa Ubangiji shi ne Allah a sama da kuma a ƙasa. Babu wani kuma. 40 Ku kiyaye ƙa’idodi da umarnai, waɗanda nake ba ku a yau, domin zaman lafiyarku da kuma na zuriyarku bayan ba ku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.
Biranen mafaka
41 Sa’an nan Musa ya keɓe birane uku gabas da Urdun, 42 waɗanda duk wanda ya yi kisankai, in ba da gangan ba ne ya kashe maƙwabcinsa, wanda babu ƙiyayya tsakaninsu a dā, zai iya gudu zuwa. Zai iya gudu zuwa cikin ɗaya daga waɗannan birane, yă tsira da ransa. 43 Biranen kuwa su ne, Bezer a dutsen hamada, don mutanen Ruben; Ramot Gileyad, don mutanen Gad; da kuma Golan a Bashan, don mutanen Manasse.
Gabatarwa ga doka
44 Wannan ita ce dokar da Musa ya sa a gaban Isra’ilawa. 45 Waɗannan su ne farillai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Musa ya ba su, sa’ad da suka fito daga Masar. 46 Sa’ad da suke a kwari kusa da Bet-Feyor, gabas da Urdun, a ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, da Musa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi sa’ad da suka fito daga Masar. 47 Suka mallaki ƙasarsa da kuma ƙasar Og sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa, gabas da Urdun. 48 Wannan ƙasa ta tashi daga Arower a kewayen Kwarin Arnon zuwa Dutsen Siyon* (wato, Hermon), 49 ya kuma haɗa da dukan Araba gabas da Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga.
* 4:48 Da Ibraniyanci; Siriyak (dubi kuma M Sh 3.9) Siriyon 4:49 Wato, Bahar Maliya