28
Albarku don biyayya
In kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuka bi dukan umarnan da na ba ku a yau, Ubangiji Allahnku zai sa ku bisa dukan al’ummai a duniya. Dukan waɗannan albarku za su sauko muku, su zama naku, in kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku.
Za ku zama masu albarka a cikin birni, za ku kuma zama masu albarka har a ƙauye.
’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka ma hatsin gonakinku da kuma ’ya’yan dabbobinku, wato, ’ya’yan shanu da ’yan tumakinku.
Za a albarkaci kwandonku da kwanon kwaɓan kullunku.
Za ku zama masu albarka sa’ad da kuka shiga, za ku kuma zama masu albarka sa’ad da kuka fita.
A gabanku, Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gāban da za su taso suna gāba da ku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.
Ubangiji zai aika da albarka a rumbunanku da kuma a bisa kome da kuka sa hannunku a kai. Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a ƙasar da yake ba ku.
Ubangiji zai kafa ku kamar mutanensa masu tsarki, kamar yadda ya yi alkawari da rantsuwa, in kun kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi tafiya a hanyoyinsa. 10 Sa’an nan dukan mutane a duniya za su ga cewa ana kiranku da sunan Ubangiji, za su kuwa ji tsoronku. 11 Ubangiji zai azurta ku sosai, a ’ya’yan cikinku, a ’ya’yan dabbobinku da kuma a hatsin gonarku, a cikin ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku.
12 Ubangiji zai buɗe sammai, wurin ajiyarsa mai yalwa, don yă aika da ruwan sama a gonarku a lokacinsa, yă kuma albarkaci dukan aikin hannuwanku. Za ku ba wa al’ummai masu yawa rance, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba. 13 Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. In kun mai da hankali ga umarnan Ubangiji Allahnku da nake ba ku a wannan rana, kuka kuma lura, kuka bi su, kullum za ku kasance a bisa, ba a ƙasa ba. 14 Kada ku kauce zuwa dama ko zuwa hagu daga umarnan da na ba ku a yau, har ku bi waɗansu alloli kuna yin musu sujada.
La’ana don rashi biyayya
(Firistoci 26.14-46)
15 Amma fa, in ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba, ba ku kuma lura kun bi dukan umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau ba, dukan la’anan nan za su zo a bisanku, su kuma same ku.
16 Za ku zama la’anannu a birni da kuma a ƙauye.
17 Za a la’anta kwandonku da kwanon kwaɓan kullunku.
18 Za a la’anta ’ya’yan cikinku, haka ma hatsin gonarku, da ’ya’yan shanunku da ’yan tumakinku.
19 Za a la’anta ku sa’ad da kuka shiga da sa’ad da kuka fita.
20 Ubangiji zai aiko muku da la’ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni.* 21 Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za tă manne muku, tă cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta. 22 Ubangiji zai buga ku da cuta mai lalacewa, da zazzaɓi, da ƙuna, da zafin rana, da fāri, da burtuntuna, da fumfuna, waɗanda za su azabtar da ku sai kun hallaka. 23 Girgijen da yake bisanku zai zama tagulla, ƙasar da take ƙarƙashinku za tă zama ƙarfe. 24 Ubangiji zai juye ruwan saman ƙasarku yă zama ƙura da gari; zai sauko daga gizagizai har sai kun hallaka.
25 Ubangiji zai sa a rinjaye ku a gaban abokan gābanku. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya. 26 Gawawwakinku za su zama abincin dukan tsuntsayen sarari da namun duniya, ba kuwa wanda zai kore su. 27 Ubangiji zai buge ku da maruran Masar, da ƙazuwa, da kuma ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba 28 Ubangiji zai buge ku da hauka, makanta, da rikicewar hankali. 29 Da tsakar rana za ku riƙa lallubawa kamar makaho. Za ku zama marasa nasara a cikin kome da kuka yi; kowace rana za a zalunce ku, a kuma yi muku ƙwace, ba tare da wani ya cece ku ba.
30 Za ku yi tashin yarinya, amma wani ne zai ɗauke ta yă kwana da ita. Za ku gina gida amma wani ne zai zauna a ciki. Za ku shuka inabi, amma ba za ku ma fara jin daɗin ’ya’yansa ba. 31 Za a yanka sanku a idanunku, amma ba za ko ci wani abu a cikinsa ba. Za a ƙwace jakinku ƙiri-ƙiri, amma ba za a mayar muku da shi ba. Za a ba da tumakinku ga abokan gābanku, kuma ba kowa da zai cece su. 32 Za a ba da ’ya’yanku maza da mata ga wata al’umma, za ku kuma yi ta zuba idanunku kuna neman su kullayaumi, amma a banza, domin ba ku da ikon yin kome. 33 Mutanen da ba ku sani ba za su ci kayan gonarku da amfanin wahalarku, za a yi ta cucinku, ana kuma danne ku kullum. 34 Abubuwan da za ku gani za su sa ku yi hauka. 35 Ubangiji zai buge gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai masu zafi da ba za a iya warkar da su ba, za su yaɗu daga tafin ƙafafu zuwa bisa kanku.
36 Ubangiji zai kore ku, ku da sarkin da kuka naɗa a bisanku zuwa al’ummar da ku, ko kakanninku ba su sani ba. A can za ku yi wa waɗansu alloli sujada, allolin itace da na dutse. 37 Za ku zama abin ƙi, abin dariya, da kuma abin habaici ga dukan al’ummai inda Ubangiji zai kore ku zuwa.
38 Za ku shuka iri da yawa a gona, amma za ku girbe kaɗan, domin fāra za su cinye su. 39 Za ku shuka inabi ku kuma yi musu banƙasa, amma ba za ku sha ruwan inabin ba, domin tsutsotsi za su cinye su. 40 Za ku kasance da itatuwan zaitun ko’ina a ƙasarku, amma ba za ku yi amfani da mansu ba, domin ’ya’yan zaitun za su kakkaɓe. 41 Za ku haifi ’ya’ya maza da mata, amma za su zama naku ba, domin za a kai su bauta. 42 Tarin fāra za su mamaye dukan itatuwanku da kuma hatsin gonarku.
43 Baƙin da suke tare da ku, za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya-baya. 44 Za su ba ku bashi, amma ba za ku ba su bashi ba. Za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya.
45 Dukan waɗannan la’anoni za su sauko a kanku. Za su bi ku, su same ku, sai an hallaka ku, domin ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da ya ba ku ba. 46 Za su zama alamu da al’ajabi gare ku da kuma zuriyarku har abada. 47 Gama ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da farin ciki da kuma murna a lokacin wadata ba, 48 saboda haka a cikin yunwa da ƙishirwa, cikin tsiraici da mugun talauci, za ku bauta wa abokan gāban da Ubangiji ya aiko muku. Zai sa karkiyar ƙarfe a wuyanku har sai ya hallaka ku ƙaf.
49 Ubangiji zai kawo al’umma daga nesa, daga iyakar duniya, ta sauko a kanku kamar gaggafa, al’ummar da ba ku san yarenta ba, 50 al’umma mai zafin hali wadda ba ta ba wa tsofaffi girma, kuma ba ta tausayin yara. 51 Za su cinye ’ya’yan dabbobinku da hatsin gonarku sai an hallaka ku. Ba za su rage ko ƙwayar hatsi, ko sabon ruwan inabi, ko mai ba, ba kuwa za a bar ’yan tumakinku ba, sai an lalatar da ku. 52 Za su kuwa kewaye ku a dukan garuruwanku, har sai katangarku masu tsayi wadda kuke dogara gare su, sun fāɗi ko’ina a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.
53 Saboda wahalar da abokan gābanku za su gasa muku a lokacin kwanto, za ku ci ’ya’yan cikinku, naman ’ya’yanku maza da mata waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku. 54 Kai, har da mutumin da ya fi hankali da kuma kirki a cikinku, ba zai ji tausayi ɗan’uwansa, ko matar da yake ƙauna, ko ’ya’yansa da suka ragu ba, 55 ba kuwa zai ba waninsu wani naman ’ya’yansa da yake ci ba. Gama dukan abin da ya rage masa ke nan saboda wahalar da abokan gābanku za su gasa muku a lokacin da ake kwanton wa dukan biranenku. 56 Mace mafi hankali da kuma kirki a cikinku, kai, mafi hankali da kirki da ba ta ma karambanin taɓa ƙasa da tafin ƙafarta, za tă hana wa mijinta da take ƙauna, da kuma ɗanta, ko ’yarta abinci. 57 A ɓoye za tă ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da ’ya’yan da za tă haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da abokan gābanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.
58 In ba ku lura kuka bi dukan kalmomi wannan doka, waɗanda an rubuta a wannan littafi ba, ba ku kuma girmama wannan suna mai ɗaukaka da kuma mai banrazana na Ubangiji Allahnku ba, 59 Ubangiji zai aika da annoba masu zafi a kanku da zuriyarku, masifu masu zafi waɗanda za su daɗe, da mugayen cututtuka waɗanda ba sa kawuwa. 60 Zai kawo muku dukan cututtukan Masar da kuke tsoro, za su kuwa manne muku. 61 Ubangiji kuma zai kawo muku kowane irin ciwo da masifar da ba a rubuta a cikin wannan Littafin Doka ba, har sai an hallaka ku. 62 Ku da kuke da yawa kamar taurari a sarari za ku ragu ku zama kaɗan, domin ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba. 63 Kamar yadda ya gamshi Ubangiji ya sa kuka yi arziki kuka kuma ƙaru, haka zai gamshe shi yă lalatar yă kuma hallaka ku. Za a tumɓuke ku daga ƙasar da kuke shiga ku mallaka.
64 Sa’an nan Ubangiji zai watsar da ku cikin dukan al’ummai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. A can za ku bauta waɗansu alloli, allolin itace da na dutse, waɗanda ko ku, ko kakanninku, ba ku sani ba. 65 A cikin waɗancan al’ummai ba za ku sami hutu ba, ba wurin hutu wa tafin ƙafanku. A can Ubangiji zai sa fargaba a zuciyarku, yă sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu. 66 Za ku yi zama cikin damuwa kullum, cike da tsoro, dare da rana, ba tabbacin abin da zai faru da ranku. 67 Da safe za ku ce, “Da ma yamma ne!” Da yamma kuma ku ce, “Da ma safiya ce!” Saboda tsoron da ya cika zukatanku da kuma abubuwan da idanunku za su gani. 68 Ubangiji zai komar da ku cikin jiragen ruwa zuwa Masar, tafiyar da na ce kada ku ƙara yi. A can za ku ba da kanku don sayarwa ga abokan gābanku a matsayin bayi maza da mata, amma ba wanda zai saye ku.
* 28:20 Da Ibraniyanci ni.