29
Sabuntawar alkawari
Waɗannan su ne sharuɗan alkawarin da Ubangiji ya umarci Musa yă yi da Isra’ilawa a Mowab, wato, ban da alkawarin da ya yi da su a Dutsen Horeb.
Sai Musa ya tara dukan Isra’ila, ya ce musu,
 
Idanunku sun ga dukan abin da Ubangiji ya yi a Masar ga Fir’auna, ga kuma dukan shugabanninsa da kuma ga dukan ƙasarsa. Da idanunku kun ga waɗannan gwaje-gwaje, waɗannan alamu masu banmamaki, da al’ajabai masu girma. Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku hankalin ganewa, ko idanun da za su gani, ko kunnuwan da za su ji ba. Shekaru arba’in da na jagorance ku cikin hamada, tufafinku ba su yage ba, haka kuwa takalman da suke a ƙafafunku. Ba ku ci burodi ba, ba ku kuwa sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa jiri ba. Ya yi haka don ku san cewa shi ne Ubangiji Allahnku.
Sa’ad da kuka kai wannan wuri, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan, suka fito don su yi yaƙi da mu, amma muka ci su da yaƙi. Muka ƙwace ƙasarsu, muka ba da ita gādo ga mutanen Ruben, mutanen Gad, da kuma rabin mutanen Manasse.
Saboda haka sai ku kiyaye, ku bi sharuɗan wannan alkawari, don ku yi nasara a cikin kome da kuke yi. 10 Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabanninku da manyan mutanenku, dattawanku da hafsoshinku, da kuma dukan sauran mutanen Isra’ila, 11 tare da ’ya’yanku da matanku, da baƙin da suke zama sansanoninku, har ma da waɗanda suke muku faskare, da waɗanda suke ɗiba muku ruwa. 12 Kuna tsaye a nan don ku yi alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji yake yi ta wurin rantsuwa da ku a wannan rana, 13 don yă mai da ku jama’arsa yau, shi kuwa yă zama Allahnku kamar yadda ya yi muku alkawari, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub. 14 Ina yin wannan alkawari da rantsuwar, ba da ku kaɗai da 15 kuke tsattsaye a nan tare da mu a yau a gaban Ubangiji Allahnmu ba, amma har da waɗanda ba sa nan yau.
16 Ku kanku kun san yadda muka yi zama a Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al’ummai muka wuce. 17 A cikinsu, kun ga siffofi masu banƙyama da gumaka na itace da dutse, na azurfa da zinariya. 18 Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, tă koma ga bauta wa gumakan waɗannan al’ummai. Kada a sami wani tushe mai ba da ’ya’ya masu dafi, masu ɗaci a cikinku.
19 Idan kuma wani mutum ya ji kalmomi na wannan rantsuwa, ya kuma sa wa kansa albarka yana tunani cewa, “Ba abin da zai same ni, ko da na nace a taurinkaina.” Wannan zai jawo lalacewar dukan Isra’ila tare da kai. 20  Ubangiji ba zai gafarce shi ba, fushinsa da kishinsa za su ƙuna a kan wannan mutum. Dukan la’anonin da aka rubuta a wannan littafi za su fāɗo a kansa, Ubangiji kuwa zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama. 21  Ubangiji zai ware shi daga dukan kabilan Isra’ila don yă hukunta shi bisa ga dukan la’anonin alkawarin da aka rubuta a wannan Littafin Doka.
22 Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato, ’ya’yan da za su gāje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji ya buge ta da su. 23 Ƙasar gaba ɗaya za tă zama gishiri mai ƙuna marar amfani da kuma kibiritu, babu shuki, babu abin da yake tsirowa, babu itatuwan da suke girma a cikinta. Za tă zama kamar yadda aka hallaka Sodom da Gomorra, Adma da Zeboyim, waɗanda Ubangiji ya hallaka cikin zafin fushinsa. 24 Dukan al’ummai za su yi tambaya su ce, “Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya jawo wannan fushi mai tsanani haka?”
25 Amsar kuwa za tă zama, “Wannan ya zama haka domin wannan mutane, sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, alkawarin da ya yi da su sa’ad da ya fitar da su daga Masar. 26 Sun juya, suka bauta wa waɗansu alloli, suka rusuna musu, allolin da ba su sani ba, allolin da Ubangiji bai ba su ba. 27 Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan wannan ƙasa, har ya kawo dukan la’anoni da aka rubuta a wannan littafi a kanta. 28 Cikin zafin fushi da babbar hasala Ubangiji ya tumɓuke su daga ƙasarsu, ya watsar da su cikin wata ƙasa dabam, kamar yadda suke a yau.”
29  Ubangiji Allahnmu bai bayyana abubuwa na yanzu da na nan gaba ba, amma ya umarce mu mu kiyaye kalmomin dokar da ya ba mu, mu da kuma ’ya’yanmu har abada.