10
Kamar yadda matattun ƙudaje sukan ɓata ƙanshin turare,
haka ’yar wauta takan ɓata hikima da daraja.
Zuciyar mai hikima takan karkata ga yin abin da yake daidai,
amma zuciyar wawa takan karkata ga yin mugun abu.
Ko yayinda yake tafiya a kan hanya
wawa yakan nuna cewa ba shi da hankali,
yakan nuna wa kowa wawancinsa.
In hankalin mai mulki ya tashi game da kai,
kada ka bar inda kake,
gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.
 
Akwai muguntar da na gani a duniya,
irin kuskuren da yake fitowa daga masu mulki.
Akan sa wawaye a manyan matsayi,
yayinda masu arziki suna ƙarƙashi.
Na taɓa ganin bayi a kan dawakai,
yayinda ’ya’yan sarki suna takawa a ƙasa kamar bayi.
 
Duk wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki;
duk wanda ya rushe katanga, shi maciji zai sara.
Duk mai farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni;
duk mai faskaren itace yana cikin hatsarinsu.
 
10 In gatari ya dakushe
ba a kuma wasa shi ba,
dole a yi amfani da ƙarfi da yawa,
amma ƙwarewa yana kawo nasara.
 
11 In maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi,
ina amfanin maganin?
 
12 Kalmomi daga bakin mai hikima alheri ne,
amma maganganun wawa za su hallaka shi.
13 Farkon maganarsa wauta ce,
ƙarshenta kuma takan zama muguwar hauka,
14 wawa kuma yakan yi ta surutu.
 
Ba wanda ya san abin da zai zo
wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?
 
15 Aikin wawa yakan gajiyar da shi,
har bai san hanyar zuwa gari ba.
 
16 Kaitonki, ya ke ƙasa wadda sarkinki bawa ne*
wadda kuma hakimanta ke ta shagali tun da safe.
17 Mai albarka ce, ya ke ƙasa wadda sarkinki haifaffen gidan sarauta ne,
wadda hakimanta suke samun abincinsu a daidai lokacin
don samun ƙarfi ba don buguwa ba.
 
18 In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa,
in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo.
 
19 Akan shirya abinci don jin daɗi,
ruwan inabi kuwa don faranta zuciya,
amma kuɗi ne amsar kome.
 
20 Kada ka zagi sarki ko da a cikin tunaninka ne,
ko ka zagi mai arziki ko da a ɗakin kwananka ne,
gama tsuntsun sararin sama zai iya ɗauki maganarka,
tsuntsu mai fikafikai zai sanar da abin da ka ce.
* 10:16 Ko kuma sarki yaro ne