11
Burodi a bisa ruwaye
Ka jefa burodinka a bisa ruwaye,
gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa.
Ka raba abin hannunka ga mutum bakwai, I, har ma takwas,
gama ba ka san bala’in da zai auko wa ƙasar ba.
 
In gizagizai sun cika da ruwa,
sukan zub da ruwan sama bisa duniya.
Itace ya fāɗi, ko wajen kudu ne, ko wajen arewa,
inda ya fāɗi a nan zai kwanta.
Duk mai la’akari da iska, ba zai yi shuka ba,
mai la’akari da gizagizai kuma, ba zai yi girbi ba.
 
Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba,
ko yadda aka siffanta jiki a cikin mahaifiya,
haka ba za ka fahimci aikin Allah
Mahaliccin dukan abubuwa ba.
 
Ka shuka irinka da safe,
da yamma kuma kada ka janye hannunka,
gama ba ka san wanda zai yi albarka ba,
ko wannan ko wancan,
ko kuma duka biyunsu su yi albarka.
Ka tuna da mahaliccinka a ƙuruciyarka
Haske da yana da kyau,
abu mai kyau ne kuma idanu su dubi rana.
Kome tsawon rayuwar mutum,
bari yă more su duka.
Amma bari kuma yă tuna da kwanakin duhu,
gama su ma za su yi yawa.
Duk abin da zai faru ba shi da amfani.
 
Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka,
bari zuciyarka kuma tă yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka.
Ka bi shawarar zuciyarka
da kuma duk abin da idanunka suka gani,
amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan
Allah zai shari’anta ka.
10 Saboda haka, ka fid da tsoro daga zuciyarka
ka kakkaɓe duk wani abin da ya dami rayuwarka,
gama ƙuruciya da ƙarfi ba su da amfani.