10
Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa;
ya fitar da ’ya’ya wa kansa.
Yayinda ’ya’yan suka ƙaru,
ya gina ƙarin bagadai;
da ƙasarsa ta wadata,
ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.
Zuciyarsu masu ruɗu ne,
yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu.
Ubangiji zai rushe bagadansu
yă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu.
 
Sa’an nan za su ce, “Ba mu da sarki
domin ba mu girmama Ubangiji ba.
Amma ko da ma muna da sarki,
me zai yi mana?”
Sun yi alkawura masu yawa,
suka yi rantsuwar ƙarya
da kuma yarjejjeniyoyi;
saboda haka ƙararraki suka taso
kamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona.
Mutanen da suke zama a Samariya suna tsoro
saboda gunki maraƙin Bet-Awen.*
Mutanensa za su yi makokinsa,
haka ma firistocinsa matsafa,
waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa,
don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta.
Za a ɗauke shi a kai Assuriya
kamar gandu wa babban sarki.
Efraim zai sha kunya;
Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa.
Samariya da sarkinta za su ɓace
kamar kumfa a bisa ruwaye.
Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta
zunubin Isra’ila ne.
Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma
su rufe bagadansu.
Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!”
Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!”
 
“Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra’ila,
a can kuwa kuka ci gaba.
Yaƙi bai cimma
masu aikata mugunta a Gibeya ba?
10 Sa’ad da na ga dama, zan hukunta su;
al’ummai za su taru su yi gāba da su
don su daure su saboda zunubansu da suka riɓanya.
11 Efraim horarriyar karsana ce
mai son sussuka;
saboda haka zan sa karkiya
a kyakkyawan wuyanta.
Zan bi da Efraim,
Dole Yahuda yă yi noma,
dole kuma Yaƙub yă ja garman noma.
12 Ku shuka wa kanku adalci,
ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa,
ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba;
gama lokaci ne na neman Ubangiji,
sai ya zo
ya zubo adalci a kanku.
13 Amma kun shuka mugunta,
kuka girbe mugu
kuka ci ’ya’yan ruɗu.
Domin kun dogara da ƙarfinku
da kuma a jarumawanku masu yawa,
14 hayaniyar yaƙi za tă tashi gāba da mutanenku,
saboda a ragargaza kagaranku,
kamar yadda Shalman ya ragargaza Bet-Arbel a ranar yaƙi,
sa’ad da aka fyaɗa uwaye tare da ’ya’yansu da ƙasa.
15 Haka zai faru da kai, ya Betel,
domin muguntarka ta yi yawa.
Sa’ad da wannan rana ta zo,
za a hallaka sarkin Isra’ila ƙaƙaf.
* 10:5 Bet-Awen yana nufin gidan mugunta (suna don Betel, wanda yake nufin gidan Allah). 10:9 Ko kuwa a can aka ɗauki matsayi