9
Hukunci domin Isra’ila
Kada ku yi farin ciki, ya Isra’ila;
kada ku yi murna kamar waɗansu al’ummai.
Gama kun yi rashin aminci ga Allahnku;
kuna son hakkokin karuwa
a kowace masussuka.
Masussukai da wuraren matsin inabi ba za su ciyar da mutane ba;
sabon ruwan inabi zai kāsa musu.
Ba za su ci gaba da zama a ƙasar Ubangiji ba;
Efraim zai koma Masar
yă kuma ci abinci marar tsarki a Assuriya.
Ba za su zuba hadayun ruwan inabi ga Ubangiji ba,
ba kuwa hadayunsu za su gamshe shi ba.
Irin hadayun nan za su zama musu kamar burodin masu makoki;
duk wanda ya ci su zai ƙazantu.
Wannan abincin zai zama na kansu ne;
ba zai zo cikin haikalin Ubangiji ba.
 
Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar bukukkuwarku,
a ranakun bikin Ubangiji?
Ko da sun kuɓuta daga hallaka,
Masar za tă tattara su,
Memfis kuma za tă binne su.
Sarƙaƙƙiya za tă mamaye kayan azurfansu,
ƙayayyuwa su tsiro a cikin tentunansu.
Kwanakin hukunci suna zuwa,
kwanakin ba da lissafi suna a kusa.
Bari Isra’ila su san da wannan.
Saboda zunubanku sun yi yawa
ƙiyayyarku kuma ta yi yawa,
har ake ɗauka annabi wawa ne,
mutumin da aka iza kuwa mahaukaci.
Annabi, tare da Allahna,
su ne masu tsaro a bisa Efraim,*
duk da haka tarko na jiransa a dukan hanyoyi,
da kuma ƙiyayya a cikin gidan Allahnsa.
Sun nutse da zurfi cikin lalaci,
kamar a kwanakin Gibeya.
Allah zai tuna da muguntarsu
yă kuma hukunta su saboda zunubansu.
 
10 “Sa’ad da na sami Isra’ila,
ya zama kamar samun inabi a hamada;
sa’ad da na ga kakanninku,
ya zama kamar ganin ’ya’yan itace na farko a itacen ɓaure.
Amma sa’ad da suka zo Ba’al-Feyor,
suka keɓe kansu wa gumaka bankunya
sai suka zama abubuwan banƙyama kamar abubuwan da suke ƙauna.
11 Darajar Efraim za tă yi firiya tă tafi kamar tsuntsu,
ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki.
12 Ko da sun yi renon ’ya’ya,
zan sa su yi baƙin cikin kowannensu.
Kaitonsu
sa’ad da na juya musu baya!
13 Na ga Efraim, kamar birnin Taya,
da aka kafa a wuri mai daɗi.
Amma Efraim zai fitar
da ’ya’yansu ga masu yanka.”
 
14 Ka ba su, ya Ubangiji
Me za ka ba su?
Ka ba su mahaifar da za su yi ɓarin ciki
da busassun nono.
 
15 “Saboda dukan muguntarsu a Gilgal,
na ƙi su a can.
Saboda ayyukansu na zunubi,
zan kore su daga gidana.
Ba zan ƙara ƙaunace su ba;
dukan shugabanninsu ’yan tawaye ne.
16 An ka da Efraim,
saiwarsu ta bushe,
ba sa ba da amfani.
Ko da sun haifi ’ya’ya
zan kashe waɗanda suka fi ƙauna.”
 
17 Allahna zai ƙi su
saboda ba su yi masa biyayya ba;
za su zama masu yawo a cikin al’ummai.
 
* 9:8 Ko kuwa Annabi ne mai tsaro a bisa Efraim, mutanen Allahna