12
Jerin sarakunan da aka ci da yaƙi
Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba.
 
Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon.
Ya yi mulki daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa, Kogin Yabbok, wanda yake iyakar Ammonawa. Wannan ya haɗa da rabin Gileyad.
Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga.
Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.
Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.
 
Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.
 
Waɗannan su ne sarakuna da kuma ƙasashen da Yoshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammancin Urdun, daga Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa Seyir. Yoshuwa ya raba ƙasarsu ta zama gādo ga Isra’ilawa bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila. Ƙasar ta haɗa da ƙasar kan tudu, filayen arewanci, Araba, gangaren Dutse, da jejin, da kuma Negeb, wato, ƙasashen Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa.
 
Sarkin Yeriko, ɗaya
sarkin Ai (kusa da Betel), ɗaya
10 sarkin Urushalima, ɗaya
sarkin Hebron, ɗaya
11 sarkin Yarmut, ɗaya
sarkin Lakish, ɗaya
12 sarkin Eglon, ɗaya
sarkin Gezer, ɗaya
13 sarkin Debir, ɗaya
sarkin Bet-Gader, ɗaya
14 sarkin Horma, ɗaya
sarkin Arad, ɗaya
15 sarkin Libna, ɗaya
sarkin Adullam, ɗaya
16 sarkin Makkeda, ɗaya
sarkin Betel, ɗaya
17 sarkin Taffuwa, ɗaya
sarkin Hefer, ɗaya
18 sarkin Afek, ɗaya
sarkin Sharon, ɗaya
19 sarkin Madon, ɗaya
sarkin Hazor, ɗaya
20 sarkin Shimron Meron, ɗaya
sarkin Akshaf, ɗaya
21 sarkin Ta’anak, ɗaya
sarkin Megiddo, ɗaya
22 sarkin Kedesh, ɗaya
sarkin Yokneyam a Karmel, ɗaya
23 sarkin Dor (A Nafot Dor), ɗaya
sarkin Goyim a Gilgal, ɗaya
24 sarki Tirza, ɗaya.
 
Duka-duka dai sarakuna talatin da ɗaya ne.