13
Ƙasar da ba a riga an ƙwace ba tukuna
1 Sa’ad da Yoshuwa ya tsufa, Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi kuma akwai sauran ƙasa mai fāɗi da ba ku riga kun mallaka ba.
2 “Ga ƙasar da ta rage,
“dukan yankunan Filistiyawa da na Geshurawa.
3 Daga Kogin Shihor a gabashin Masar zuwa sashen Ekron a arewa, dukan wannan ƙasa ana lissafta ta a cikin ƙasar Kan’aniyawa, ko da yake tana a sashen da sarakuna biyar na Filistiyawa na Gaza, Ashdod, Ashkeloniyawa, Gat da Ekron;
na Awwiyawa.
4 Daga wajen kudu kuma,
dukan ƙasar Kan’aniyawa ce. Iyakarta a arewa ta fara daga Ara ta Sidoniyawa har zuwa Afek, ta zarce har zuwa iyakar Amoriyawa;
5 da ƙasar Gebaliyawa;
da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba’al-Gad a gindin Dutsen Hermon zuwa Lebo Hamat.
6 “Dukan mazauna kan yankunan tuddai daga Lebanon zuwa Misrefot Mayim, wato, dukan Sidoniyawa, ni da kaina zan kore su a gaban Isra’ilawa. Ka tabbata ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka,
7 ka raba ta tă zama gādo wa kabilu tara da kuma rabin kabilar Manasse.”
Raba ƙasar da take gabashin Urdun
8 Rabin kabilar Manasse, mutanen Ruben da mutanen Gad suka karɓi rabonsu na gādo wanda Musa ya ba su a gabashin Urdun. Abin da Musa bawan Ubangiji ya ba su ke nan.
9 Wannan ya tashi daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, ya kuma haɗa da ƙasar da take tudun Medeba har zuwa Dibon,
10 da dukan garuruwan Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon, har zuwa iyakar Ammonawa.
11 Haɗe da Gileyad, inda mutanen Geshur da Ma’aka suke. Dukan Dutsen Hermon, da dukan Bashan har zuwa Saleka,
12 wato, dukan masarautar Og a Bashan, wanda ya yi mulkin Ashtarot da Edireyi, yana cikin waɗanda suke na ƙarshe da ba a kashe ba a cikin Refahiyawa. Musa ya ci su da yaƙi, ya ƙwace ƙasarsu.
13 Amma Isra’ilawa ba su kori mutanen Geshur da Ma’aka ba, saboda haka suka ci gaba da zama cikin Isra’ilawa har wa yau.
14 Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa da ake miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.
15 Ga abin da Musa ya ba kabilar Ruben bisa ga iyalansu.
16 Abin da ya kama daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba
17 zuwa Heshbon, da dukan garuruwan kan tudu, haɗe da Dibon, Bamot Ba’al, Bet-Ba’al-Meyon,
18 Yahza, Kedemot, Mefa’at,
19 Kiriyatayim, Sibma, Zeret Shahar kan tudu cikin kwari,
20 Bet-Feyor, gangaren Fisga da Bet-Yeshimot,
21 dukan garuruwan da suke kan tudu da dukan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Musa ya yi nasara da shi, da shugabannin Midiyawa, wato, Ewi, Rekem, Zur, Hur, da Reba, sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.
22 Ƙari a kan waɗanda aka kashe a yaƙi, Isra’ilawa suka kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi don yana duba.
23 Gefen Urdun shi ne iyakar mutanen Ruben. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon mutanen Ruben, bisa ga iyalansu.
24 Ga abin da Musa ya ba kabilar Gad, bisa ga iyalansu.
25 Yankin ƙasarsu ya ƙunshi Yazer, da dukan garuruwan Gileyad, da rabin ƙasar Ammonawa har zuwa Arower kusa da Rabba,
26 da kuma daga Heshbon zuwa Ramat Mizfa da Betonim, da kuma daga Mahanayim zuwa sashen Debir,
27 kuma a cikin kwari, Bet-Haram, Bet-Nimra, Sukkot da Zafon da kuma sauran masarautar Sihon sarkin Heshbon (gabashin Urdun, abin da ya kama har zuwa ƙarshen Tekun Kinneret).
28 Waɗannan garuruwan da ƙauyukansu duka, gādon mutanen Gad ne, bisa ga iyalansu.
29 Ga abin da Musa ya ba rabin kabilar Manasse, wato, wa rabin zuriyar Manasse, bisa ga iyalansu.
30 Abin da ya miƙe daga Mahanayim haɗe da dukan Bashan, da gefen masarautar Og sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,
31 da rabin Gileyad, da Ashtarot, Edireyi (biranen sarki Og a Bashan).
Wannan shi ne rabon da zuriyar Makir ɗan Manasse suka samu, domin rabin ’ya’yan Makir maza, bisa ga iyalansu.
32 Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun kusa da Yeriko.
33 Amma Musa bai ba kabilar Lawiyawa gādo ba; Ubangiji, Allah na Isra’ila, shi ne gādonsu kamar yadda ya yi musu alkawari.