11
Wuta daga wurin Ubangiji
Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai. Sai wuta daga Ubangiji ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone waɗansu wurare na sansanin. Da jama’ar suka yi wa Musa kuka, sai ya yi addu’a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu. Saboda haka aka kira wannan wuri Tabera, gama a wurin ne wuta daga Ubangiji ta ƙuna a cikinsu.
Makware daga Ubangiji
Wata rana, baƙin da suke cikinsu, suka fara kwaɗayin waɗansu abinci, har suka sa Isra’ilawa suka fara kuka, suna cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, haka ma kayan lambu irin su kukumba, guna, safa, albasa da kuma tafarnuwa. Amma ga shi yanzu ba mu da wani abin marmari; in ba wannan Manna ba!”
Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuma kamar ƙaro ne. Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa a dutsen niƙa, ko kuwa su daka a turmi. Su dafa, ko su yi waina da ita. Ɗanɗanonta yakan yi kamar abin da aka yi da man zaitun. Sa’ad da raɓa tana saukowa da dad dare a kan sansani, Manna ma takan sauko.
10 Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko’ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar tentinsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai, sai Musa ya damu. 11 Sai ya ce wa Ubangiji, “Me ya sa ka kawo wannan damuwar a kan bawanka? Me na yi da ya ɓata maka rai har ka ɗora dukan nauyin mutanen nan a kaina? 12 Ni ne na yi cikin dukan mutanen nan? Ni ne na haife su? To, me ya sa ka ce in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka yi alkawari da rantsuwa za ka ba wa kakanninsu? 13 Ina ne zan sami nama in waɗannan mutane? Sun dinga yin mini kuka suna cewa ‘Ka ba mu nama mu ci!’ 14 Ba zan iya ɗaukan dukan mutanen nan ni kaɗai ba, nauyin ya yi mini yawa. 15 In haka za ka yi da ni, ka kashe ni yanzu, in na sami tagomashi daga gare ka, kada ka bar ni in rayu in ga wannan baƙin ciki.”
16 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattaro mini dattawa saba’in daga cikin mutanen Isra’ila, waɗanda aka sani su ne dattawa da kuma shugabanni a cikin jama’a. Ka sa su zo Tentin Sujada, su tsaya a can tare da kai. 17 Zan sauko in yi magana da kai a can, zan kuma ɗauki Ruhun da yake kanka in mai da shi wajensu. Za su taimake ka ɗaukan nauyin mutane, don yă zama ba kai kaɗai ba ne mai ɗaukan kaya.
18 “Ka gaya wa mutane, ‘Ku tsarkake kanku don gobe, za ku ci nama. Ubangiji ya ji ku sa’ad da kuka yi kuka cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! Ai, da ba mu da damuwa, gama lokacin da muke zama cikin Masar ba mu da damuwa!” Yanzu Ubangiji zai ba ku nama, za ku kuma ci. 19 Ba za ku ci shi na kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko kuma kwana ashirin kaɗai ba, 20 amma za ku ci har na wata guda cur, sai ya gundure ku a hanci har ku yi ƙyamarsa, domin kun ƙi Ubangiji wanda yake cikinku, kuka yi kuka a gabansa, kuna cewa, “Don me ma muka bar ƙasar Masar?” ’ ”
21 Amma Musa ya ce, “Ga ni a cikin mutane dubu ɗari shida tafe tare da ni, kana kuma cewa, ‘Zan ba su nama su ci har wata guda cur!’ 22 Za su ma sami isashe in har aka yanka musu garkuna tumaki da na shanu? Za su sami isashe in aka kama musu dukan kifin teku?”
23 Ubangiji ya ce wa Musa, “Akwai abin da ya fi ƙarfina ne? Bari ka gani ko abin da na ce zan yi, zai faru ko babu.”
24 Saboda haka Musa ya fita ya gaya wa jama’a abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tattaro dattawansu saba’in, ya sa suka tsaya kewaye da Tentin Sujada.
25 Sa’an nan Ubangiji ya sauko daga girgije, ya yi magana da shi, ya kuma ɗauke Ruhun da yake kan Musa ya ɗora shi a kan dattawa saba’in nan. Sa’ad da Ruhun ya zauna a kansu, sai suka yi annabci, amma daga wannan ba su ƙara yin haka kuma ba.
26 To, fa, akwai dattawa biyu da suka kasance a sansani, wato, Eldad da Medad. Su ma an lasafta su cikin dattawan, amma ba su fita zuwa Tentin Sujada ba. Duk da haka Ruhun ya sauka a kansu, suka kuma yi annabci a cikin sansanin. 27 Wani saurayi ya sheƙa a guje zuwa wajen Musa ya ce, “Eldad da Medad suna can suna annabci a sansani.”
28 Sai Yoshuwa ɗan Nun, wanda yake mataimakin Musa tun yana saurayi, ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, Musa, ka hana su!”
29 Amma Musa ya amsa ya ce, “Kana kishi domina ne? Da ma a ce dukan mutanen Ubangiji annabawa ne, da ma a kuma ce Ubangiji ya sa Ruhunsa a kansu mana!” 30 Sai Musa da dattawan Isra’ila suka koma sansani.
31 Ana nan, sai Ubangiji ya kawo wata iska mai tsanani ta koro makware daga teku. Ta bar su birjik kewaye da sansani, tsayinsu daga ƙasa ya kai kamu biyu, misalin tafiyar nisan yini guda ta kowace fuska. 32 Dukan yini da dukan dare da kuma kashegari, mutane suka fito suka tattara makware. Ba wanda ya kāsa tara ƙasa da garwa goma. Sai suka shanya abinsu kewaye da sansanin. 33 Amma da suna cikin cin naman, tun ba su ma haɗiye ba, sai Ubangiji ya husata sosai a kan jama’ar, ya buge su da annoba mai zafi. 34 Saboda haka aka kira wannan wuri Kibrot Hatta’awa,* gama a can ne aka binne mutanen nan makwaɗaita.
35 Daga Kibrot Hatta’awa, mutane suka yi tafiya zuwa Hazerot, a can suka sauka.
* 11:34 Kibrot Hatta’awa yana nufin makabartan kwaɗayi.