12
Miriyam da Haruna sun tayar wa Musa
1 Miriyam da Haruna suka fara zargin Musa saboda matarsa ’yar ƙasar Kush da ya aura.
2 Suka ce, “Ubangiji ya yi magana ta wurin Musa ne kaɗai? Ashe, bai yi magana ta wurinmu mu ma ba?” Ubangiji kuwa ya ji wannan.
3 (Musa kuwa mutum ne mai tawali’u ƙwarai, mafi tawali’u fiye da kowane mutum a duniya.)
4 Nan da nan Ubangiji ya ce wa Musa, da Haruna da kuma Miriyam, “Ku fita ku tafi Tentin Sujada, dukanku uku.” Sai dukansu uku suka tafi.
5 Sai Ubangiji ya sauko a cikin ginshiƙin girgije; ya tsaya a bakin ƙofar Tenti, ya kira Haruna da Miriyam. Sa’ad da su biyu suka gusa gaba,
6 sai ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa,
“Duk lokacin da akwai annabin Ubangiji a cikinku,
nakan bayyana kaina gare shi cikin wahayi,
in yi magana da shi cikin mafarkai.
7 Amma ba haka nake magana da Musa bawana ba;
na sa shi yă lura da dukan jama’ata Isra’ila.
8 Da shi nake magana fuska da fuska,
a fili kuma, ba a kacici-kacici ba;
yakan ga siffar Ubangiji.
To, me ya sa ba ku ji tsoro
ku yi magana a kan bawana Musa ba?”
9 Sai fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kansu, ya kuma rabu da su.
10 Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce;
11 sai Haruna ya ce wa Musa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka hukunta mu, gama zunubin da muka yi, mun yi ne cikin wauta.
12 Kada ka sa ta zama kamar haifaffen mataccen jariri daga cikin mahaifiya wanda rabin jikin ruɓaɓɓe ne.”
13 Saboda haka sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Allah, ina roƙonka ka warkar da ita!”
14 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata miyau a fuskarta, ashe, ba za tă ji kunya har kwana bakwai ba? A fitar da ita bayan sansani kwana bakwai; bayan haka za a iya dawo da ita.”
15 Haka aka fitar da Miriyam bayan sansani kwana bakwai, mutane kuwa ba su ci gaba da tafiya ba sai da aka dawo da ita.
16 Bayan haka sai mutane suka bar Hazerot suka sauka a Hamadan Faran.