13
Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa,
amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.
 
Daga abin da ya fito leɓunan mutum ne mutum kan ji daɗin abubuwa masu kyau,
amma marar aminci yakan ƙosa ya tā-da-na-zaune-tsaye.
 
Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa,
amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci.
 
Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome,
amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.
 
Adali yana ƙin abin da yake ƙarya,
amma mugu kan jawo kunya da ƙasƙanci.
 
Adalci yakan lura da mutum mai mutunci,
amma mugunta takan sha kan mai zunubi.
 
Wani mutum yakan ɗauki kansa mai arziki ne, alhali ba shi da kome,
wani ya ɗauki kansa shi matalauci ne, alhali shi mawadaci ne ƙwarai.
 
Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa,
amma matalauci ba ya jin barazana.
 
Hasken masu adalci kan haskaka ƙwarai,
amma fitilar mugaye mutuwa take.
 
10 Girmankai kan jawo faɗa ne kawai,
amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.
 
11 Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri,
amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
 
12 Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo,
amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
 
13 Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa,
amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada.
 
14 Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne,
mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.
 
15 Fahimta mai kyau kan sami tagomashi,
amma hanyar marar aminci tana da wuya.
 
16 Kowane mai azanci yakan nuna sani,
amma wawa yakan yi tallen wawancinsa.
 
17 Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala,
amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa.
 
18 Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya,
amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.
 
19 Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai,
amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta.
 
20 Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima,
amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
 
21 Rashin sa’a kan fafare mai zunubi,
amma wadata ce ladar adali.
 
22 Mutumin kirki kan bar gādo wa ’ya’ya ’ya’yansa,
amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci.
 
23 Gonar matalauci za tă iya ba da abinci a yalwace,
amma rashin adalci kan share shi tas.
 
24 Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba,
amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.
 
25 Masu adalci sukan ci isashen abinci,
amma cikin mugaye na fama da yunwa.