14
Mace mai hikima kan gina gidanta,
amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.
 
Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji,
amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi.
 
Maganar wawa kan kawo sanda a bayansa,
amma leɓunan masu hikima kan tsare su.
 
Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome,
amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito.
 
Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu,
amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi.
 
Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome,
amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira.
 
Ka guji wawa,
gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.
 
Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu,
amma wautar wawaye ruɗu ne.
 
Wawaye kan yi ba’a a gyaran zunubi,
amma fatan alheri yana samuwa a cikin masu aikata gaskiya.
 
10 Kowace zuciya ta san ɓacin ranta,
kuma babu wani dabam da zai yi rabon jin daɗinsa.
 
11 Za a rushe gidan mugu,
amma tentin mai aikata gaskiya zai haɓaka.
 
12 Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum,
amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.
 
13 Ko cikin dariya zuciya takan yi ciwo,
kuma farin ciki kan iya ƙarasa a baƙin ciki.
 
14 Marasa bangaskiya za su sami sakamako cikakke saboda hanyoyinsu,
kuma mutumin kirki zai sami lada saboda nasa.
 
15 Marar azanci kan gaskata kome,
amma mai la’akari kan yi tunani game da matakinsa.
 
16 Mai hikima kan ji tsoron Ubangiji ya kuma guji mugunta,
amma wawa yana da girman kai yakan yi kome da garaje.
 
17 Mutum mai saurin fushi yakan yi ayyukan wauta,
akan kuma ƙi mai son nuna wayo.
 
18 Marar azanci kan gāji wauta,
amma mai la’akari kan sami rawanin sani.
 
19 Masu mugunta za su rusuna a gaban masu kirki,
mugaye kuma za su yi haka a ƙofofin adalai.
 
20 Maƙwabta sukan gudu daga matalauta,
amma masu arziki suna da abokai da yawa.
 
21 Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi,
amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata.
 
22 Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba?
Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci.
 
23 Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba,
amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.
 
24 Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu,
amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai.
 
25 Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka,
amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne.
 
26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,
kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.
 
27 Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai
yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.
 
28 Yawan mutane shi ne ɗaukakar sarki,
amma in ba tare da mabiya ba sarki ba kome ba ne.
 
29 Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa,
amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.
 
30 Zuciya mai salama kan ba jiki rai,
amma kishi kan sa ƙasusuwa su yi ciwo.
 
31 Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan,
amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.
 
32 Sa’ad bala’i ya auku, mugaye kan fāɗi,
amma ko a mutuwa masu adalci suna da mafaka.
 
33 Hikima tana a zuciyar mai azanci,
kuma ko a cikin wawaye takan sa a santa.
 
34 Adalci yakan ɗaukaka al’umma,
amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane.
 
35 Sarki yakan yi murna a kan bawa mai hikima,
amma bawa marar kunya kan jawo fushinsa.