13
Amnon da Tamar
1 Ana nan sai Amnon ɗan Dawuda ya fara son Tamar, kyakkyawar ’yar’uwar Absalom ɗan Dawuda.
2 Amnon ya matsu ƙwarai har abin ya sa shi ciwo saboda ƙanuwarsa Tamar. Ya gane zai zama da wuya yă sadu da Tamar ita kaɗai, gama ba ta taɓa kwana da namiji ba.
3 To, Amnon yana da wani aboki mai suna Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda. Yonadab dai mai wayo ne ƙwarai.
4 Ya tambayi Amnon ya ce, “Don me kowace safiya fuskarka a ɓace take? Kai ba yaron sarki ba ne? Faɗa mini, me ke faruwa?”
Amnon ya ce masa, “Ina son Tamar ƙanuwar wan nawa Absalom ne.”
5 Yonadab ya ce, “Je gado ka kwanta kamar ba ka da lafiya. Sa’ad da mahaifinka ya zo ganinka, sai ka ce masa, ‘Ina so ƙanuwata Tamar tă kawo mini wani abu in ci. Bari tă shirya abincin a gabana don in ganta, in kuma ci daga hannunta.’ ”
6 Sai Amnon ya kwanta sai ka ce yana ciwo. Da sarki ya zo don ganinsa, sai Amnon ya ce, “Zan so ƙanuwata Tamar tă zo tă shirya mini abinci a gabana, don in ci daga hannunta.”
7 Dawuda kuwa ya aika wa Tamar a fada, ya ce, “Ki je gidan Amnon ɗan’uwanki, ki yi masa abinci.”
8 Saboda haka Tamar ta tafi gidan ɗan’uwanta Amnon, wanda yake kwance. Ta ɗauki fulawa, ta kwaɓa, ta yi burodi a gabansa ta toya shi.
9 Sa’an nan ta juye a kasko ta ba shi burodin, amma ya ƙi ci.
Amnon ya ce, “A sa kowa yă fita daga nan.” Saboda haka kowa ya fita ya bar shi.
10 Sa’an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a nan a cikin ɗakin kwanciyata, don in ci daga hannunki.” Tamar kuwa ta ɗauki burodin da ta toya, ta kawo wa ɗan’uwanta Amnon a ciki ɗakin kwanciyarsa.
11 Amma da ta kai masa don yă ci, sai ya cafke ta ya ce, “Zo in kwana da ke, ’yar’uwata.”
12 Ta ce, “Kada ka yi wannan ɗan’uwana! Kada ka tilasta ni. Bai kamata a yi irin wannan abu a Isra’ila ba! Kada ka yi wannan mugun abu.
13 Ni fa, ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuma za ka zama kamar wani mugun wawa a Isra’ila. Ina roƙonka ka yi wa sarki magana; ba zai hana ni aurenka ba.”
14 Amma Amnon ya ƙi yă saurare ta, da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata fyaɗe.
15 Bayan ya yi lalata da ita sai Amnon ya ƙi ta da mummunan ƙiyayya. Zahiri ya ƙi ta fiye da ya ƙaunace ta. Sai Amnon ya ce mata, “Tashi, ki fita!”
16 Ta ce, “A’a! Korina zai fi muni da abin da ka riga ka yi mini.”
Amma ya ƙi yă saurare ta.
17 Sai ya kira bawansa ya ce, “Fitar da matan nan daga nan, ka rufe ƙofa.”
18 Saboda haka bawansa ya fitar da ita, ya kuma sa aka rufe ƙofa. Tana sanye da doguwar riga mai kayan ado masu tsada, gama wannan ne irin kayan da budurwai ’ya’yan sarki mata suke sawa.
19 Sai Tamar ta zuba toka a kanta, ta kuma yayyage doguwar riga mai kayan adon da take sanye da shi. Ta sa hannunta a kai, ta tafi tana kuka da ƙarfi.
20 Absalom ɗan’uwanta ya ce mata, “Amnon, ɗan’uwanki ya ɓata ki ko? To, ki yi shiru ’yar’uwata; ai, ɗan’uwanki ne. Kada wannan abu yă dame ki.” Tamar kuwa ta zauna a gidan ɗan’uwanta Absalom, zaman kaɗaici.
21 Da Sarki Dawuda ya ji dukan abin da ya faru, sai ya husata ƙwarai.
22 Absalom kuwa bai yi wa Amnon wata magana ta alheri ko ta mugunta ba; ya ƙi jinin Amnon domin ya ci mutuncin ƙanuwarsa Tamar.
Absalom ya kashe Amnon
23 Bayan shekaru biyu, sa’ad da masu askin tumakin Absalom suna Ba’al-Hazor, kusa da iyakar Efraim, sai ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza a can.
24 Sai Absalom ya je wurin sarki ya ce, “Bawanka ya sa masu askin tumaki sun zo. Ko sarki da fadawansa za su zo tare da ni?”
25 Sarki ya ce, “A’a ɗana, bai kamata dukanmu mu tafi ba; don kada nauyi yă yi maka yawa.” Absalom dai ya dāge, duk da haka sarki ya ƙi yă je, sai dai ya albarkace shi.
26 Sa’an nan Absalom ya ce, to, “In ba za ka ba, ina roƙonka bari Amnon ɗan’uwana yă zo tare da mu.”
Sarki ya ce masa, “Don me zai tafi tare da kai?”
27 Amma Absalom ya nace don sarki yă yarda, saboda haka sarki ya bar Amnon da sauran ’ya’yan sarki maza su tafi tare da shi.
28 Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.”
29 Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran ’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu.
30 Yayinda suke kan hanyarsu, sai labari ya kai kunnen Dawuda cewa, “Absalom ya kashe dukan ’ya’yan sarki maza; ko ɗayansu Absalom bai rage ba.”
31 Sai sarki ya tashi, ya yage tufafinsa, ya kuma kwanta a ƙasa; dukan bayinsa kuwa suka tsaya da rigunansu yagaggu.
32 Amma Yonadab, ɗan Shimeya ɗan’uwan Dawuda ya ce, “Kada ranka yă daɗe yă yi tunani cewa an kashe dukan ’ya’yan sarki maza; Amnon ne kaɗai ya mutu. Wannan ce niyyar Absalom tun lokacin da Amnon ya yi wa Tamar ’yar’uwansa fyaɗe.
33 Kada mai girma sarki yă damu da jita-jitan nan cewa an kashe dukan ’ya’yan sarki maza. Amnon ne kaɗai ya mutu.”
34 Ana cikin haka, sai Absalom ya gudu.
To, mutumin da yake tsaro a wannan lokaci ya ɗaga kai sai ya ga mutane da yawa a hanya, yamma da shi, suna gangarowa daga gefen tudu. Sai mai tsaron ya je ya gaya wa sarki cewa, “Na ga mutane ta wajen Horonayim, a gefen tudu.”
35 Yonadab ya ce wa Sarki, “Duba, ga ’ya’yan sarki maza sun zo; ya faru kamar dai yadda bawanka ya faɗa.”
36 Yana gama magana, sai ga ’ya’yan sarki maza suka shigo suna kuka da ƙarfi. Sarki ma da dukan bayinsa suka yi kuka mai zafi.
37 Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai ɗan Ammihud, sarkin Geshur. Amma Sarki Dawuda ya yi ta makokin ɗansa kowace rana.
38 Bayan Absalom ya gudu sai ya je wurin Geshur, ya zauna a can shekara uku.
39 Sai zuciyar sarki Dawuda ya komo kan Absalom, gama an yi masa ta’aziyya game da mutuwar Amnon.