14
Absalom ya koma Urushalima
1 Yowab, ɗan Zeruhiya ya gane cewa zuriyar sarki ta koma ga Absalom.
2 Saboda haka Yowab ya aiki wani zuwa Tekowa, ya sa a zo da wata mace mai hikima. Ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki. Ki sa rigar makoki, kada kuwa ki shafa mai. Ki yi kamar macen da ta yi kwanaki da yawa, tana makokin matattu.
3 Sa’an nan ki je wurin sarki, ki ce masa haka.” Sai Yowab ya faɗa mata duk abin da za tă faɗa.
4 Da macen da ta fito daga Tekowa ta je wajen sarki, sai ta rusuna har ƙasa don bangirma, sai ta ce, “Ka taimake ni, ya sarki!”
5 Sarki ya ce mata, “Mece ce matsalarki?”
Sai ta ce, “Tabbatacce, ni gwauruwa ce; mijina ya mutu.
6 Baiwarka tana da ’ya’ya maza biyu. Suka yi faɗa da juna a fili, kuma ba wanda yake can don yă raba su. Ɗayan ya bugi ɗayan, ya kashe shi.
7 To, ga duk iyali sun hau kan baiwarka, suna cewa, ‘Ki ba mu ɗayan da ya kashe ɗan’uwansa mu kashe don ran ɗan’uwansa da ya kashe; sa’an nan za mu hallaka magājin shi ma.’ Za su kashe garwashin wuta mai ci da nake da shi kaɗai, su bar mijina ba suna, ba jika, a duniya.”
8 Sarki ya ce wa macen, “Koma gida, zan ba da umarni a madadinki.”
9 Amma macen da ta fito daga Tekowa ta ce, “Ranka yă daɗe, sarki! Bari alhakin shari’arka yă kasance a kaina da gidan mahaifina, kai sarki da gidan mulkinka, ba ku da laifi a ciki.”
10 Sai sarki ya ce, “In wani ya yi miki magana, ki kawo shi wurina, ba zai kuwa ƙara damunki ba.”
11 Sai ta ce, “To, bari sarki yă rantse da Ubangiji Allahnsa don yă hana mai ramako yin ƙarin hallakawar da aka yi, domin kada a hallaka ɗana.”
Sai ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, babu gashi guda na ɗanki da zai fāɗi ƙasa.”
12 Sai matar ta ce, “Bari baiwarka ta ƙara yin magana sau ɗayan nan wa ranka yă daɗe.”
Ya ce, “Ki faɗa.”
13 Matar ta ce, “To, don me ka yi wa mutanen Allah irin wannan abu? Sa’ad da sarki ya ce haka, ashe, ba ka hukunta kanka ke nan ba, tun da yake sarki bai yarda ɗansa yă komo gida ba?
14 Kamar ruwan da ya zuba a ƙasa, wanda ba a iya kwasa, haka dole mu mutu. Amma Allah ba ya ɗaukan rai; a maimako, yakan ƙirƙiro hanyoyi domin mutumin da aka kora kada yă kasance yasasshe daga gare shi.
15 “Yanzu ga shi na zo don in faɗa wannan wa ranka yă daɗe sarki, don mutane sun tsorata ni. Baiwarka ta yi tunani ta ce, ‘Zan yi magana wa sarki; wataƙila yă yi abin da baiwarsa ta roƙa.
16 Wataƙila sarki zai yarda yă ceci baiwarsa daga hannun mutumin nan da yake ƙoƙari yă hallaka ni da ɗana daga gādon da Allah ya ba mu.’
17 “Yanzu kuwa baiwarka tana cewa, ‘Bari magana ranka yă daɗe sarki yă ba ni hutu, gama ranka yă daɗe sarki yana kama da mala’ikan Allah cikin rarrabe nagarta da mugunta. Bari Ubangiji Allahnka yă kasance tare da kai.’ ”
18 Sai sarki ya ce wa matar, “Kada ki ɓoye mini kome daga abin da zan tambaye ki.”
Matar ta ce, “Bari ranka yă daɗe sarki yă yi tambaya.”
19 Sarki ya ce, “Anya, babu hannun Yowab a cikin dukan wannan?”
Matar ta ce, “Muddin kana a raye, ranka yă daɗe sarki, ba wanda zai juya dama ko hagu daga wani abin da ranka yă daɗe sarki ya faɗa. I, bawanka Yowab ne ya umarce ni in yi wannan, shi ne kuma ya sa kalmomin nan a bakin baiwarka.
20 Bawanka Yowab ne ya yi haka don yă daidaita al’amura. Ranka yă daɗe yana da hikima iri ta mala’ikan Allah, ya san dukan kome da yake faruwa a ƙasar.”
21 Sarki ya ce wa Yowab, “To, da kyau, zan yi haka. Je ka, ka dawo da saurayin nan Absalom.”
22 Yowab ya rusuna har ƙasa don bangirma, ya kuma yi wa sarki kyakkyawar fata. Yowab ya ce, “Yau, bawanka ya sani ya sami tagomashi a gare ka, ranka yă daɗe sarki, gama sarki ya ji roƙon bawansa.”
23 Sa’an nan Yowab ya tafi Geshur ya dawo da Absalom Urushalima.
24 Amma sarki ya ce, “Yă tafi gidansa; kada yă zo yă gan ni.” Saboda haka Absalom ya tafi gidansa, bai kuwa je ganin sarki ba.
25 A cikin dukan Isra’ila babu wanda ake yabon kyansa kamar Absalom. Tun daga kansa har zuwa tafin ƙafansa babu tabo a jikinsa.
26 A duk sa’ad da ya aske gashin kansa (yakan aske kansa lokaci-lokaci sa’ad da ya yi masa nauyi) yakan auna shi, nauyin gashin kuwa yakan kai wajen shekel ɗari biyu a ma’aunin da ake awo.
27 Aka haifa wa Absalom ’ya’ya uku maza da ’ya mace guda. Sunanta Tamar, ta kuwa zama kyakkyawan mace ƙwarai.
28 Absalom ya zauna a Urushalima shekara biyu amma ba tare da ganin fuskar sarki ba.
29 Sai Absalom ya aika a kira masa Yowab don yă aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa. Saboda haka ya sāke aika sau na biyu, amma ya ƙi yă zo.
30 Sai ya ce wa bayinsa, “Duba, gonar Yowab tana gab da tawa, kuma yana da sha’ir a can. Ku je ku sa mata wuta.” Sai bayin Absalom suka sa wa gonar wuta.
31 Sa’an nan Yowab ya tafi gidan Absalom ya ce masa, “Me ya sa bayinka suka sa wa gonata wuta?”
32 Absalom ya ce wa Yowab, “Kai, na aika, ‘Ka zo nan don in aike ka wurin sarki ka tambaya, “Me ya sa na dawo daga Geshur? Ai, ya fi mini a ce ina can har yanzu!” ’ Yanzu kuwa, ina so in ga sarki, kuma idan na yi wani laifi, to, yă kashe ni.”
33 Saboda haka Yowab ya tafi wurin sarki ya gaya masa wannan. Sai sarki ya aika aka zo da Absalom, ya kuma rusuna da fuskarsa har ƙasa a gaban sarki. Sarki kuwa ya sumbaci Absalom.